Tuesday, 16 January 2018
Ba Hana Kiwo Ne Mafita A Nijeriya Ba !!! In Ji Shaikh Dahiru Bauchi (karanta)

Home Ba Hana Kiwo Ne Mafita A Nijeriya Ba !!! In Ji Shaikh Dahiru Bauchi (karanta)
Ku Tura A Social Media

Babban Malamin addinin Islama, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnatin tarayya a karkashin Muhammadu Buhari da ta tashi tsaye wajen kokarin shawo kan rikicin da yake addabar wasu yankunan kasar nan na rikicin Fulani Makiyaya da kuma Manoma. Yana mai bayyana cewar tashi tsaye domin shawo kan rikicin ne kawai mafita ba wai yunkurin hana Fulani kiwo ba.

Dahiru Bauchi wadda ya bayyana hakan a jiya sa’ilin ganawarsa da manema labaru a gidansa da ke Bauchi, ya ci gaba da cewa, tun usuli shi makiyayi ya saba yawo ne, don haka maganar hana shi yawun kiwo ba zai haifar da komai ba, illa wani tashin tashinan.

A don haka ne Dahiru Bauchi ya ce hanya daya tilau dai shine kawai gwamnatin tarayya ta tabbatar da samar wa makiyaya muhallan da suka dace domin yin kiwo da kuma mashayar dabbobi domin kaurace wa tashin hankali.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: