Wednesday, 24 January 2018
Anyi turereniya wajen kallon fim din Adam A Zango Gwaska Returns a kano

Home Anyi turereniya wajen kallon fim din Adam A Zango Gwaska Returns a kano
Ku Tura A Social Media
Dinbim jama'a suka garzaya babban sinima dake Ado Bayero Mall a jihar Kano domin kallon sabon shiri fim da Jarumi Adam A.Zango ya fitar ranar juma'a.

Ma'abotan fina-finai hausa kuma masoyan babban jarumin shirin "Gwaska" sun fito kwar da kwarkwatan su domin ba idanuwar su abinci.

Abun kamar a turai ganin dinbim jama'a da suke turereniya wajen karbar tikitin shiga dakin kallo.

Wannan shirin wanda Adam Zango ya taka muhimmin rawa a ciki a matsayin shi na babban jarumin shirin yana daya daga cikin fina-finai hausa da aka fitar kwana-kwana nan wanda ya samu cinciridon mutane wajen haskawa a sinima.

Goyon bayan jarumai

Suma wasu daga cikin manya-manyan jaruman masana'antar Kannywood sun garzaya wajen fim din "Gwaska Returns" domin mara ma abokin aikin su baya.

Cikin su akwai mawaki Daudu Kahutu Rarara da babban mai shirya fim Hamisu Iyantama da Yakubu Muhammed da kuma Falalu Dorayi tare da Bello Muhammed Bello wanda ya fito a matsayin jarumi cikin shirin.

A bangaren mata ita ma Maryam Gidado da sabbin shiga watau tagwayen Kannywood suma ba'a bar a baya ba wajen kallo.

Masoyan Adam Zango sun nuna masa kara tare da jinjina masa bisa kokarin da yayi wajen fitar da wannan shirin fim wanda cigaban na farko na mai taken "Gwaska".

Sai dai abin mamaki Ali Nuhu da Jama'ar sa ba'a gansu a wajen ba, ta wata majiya hakan baya rasa nasaba da takun sakar da ake a tsakanin Jaruman Guda biyu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: