Thursday, 4 January 2018
Abin da ya sa na yiwa ummah shehu tambaya kan addini shi ne? -Aminu shareef momo

Home Abin da ya sa na yiwa ummah shehu tambaya kan addini shi ne? -Aminu shareef momo
Ku Tura A Social Media

Jarumin, wanda ke gabatar da wani shiri kan fina-finai a wani gidan talbijin, ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa cewa ya tozarta wata 'yar fim a shirin nasa lokacin da ya yi mata tambayar da ake gani ba ta shafi harkar fim ba.

A cewarsa, ya yi wa Umma Shehu tambaya kan addinin Musulinci ne bayan ta bayyana masa cewa ba ta damu da kallon fina-finai ba saboda tana zuwa makaranta.

"Abin da ya sa na yi mata tambaya kan addini shi ne, na ga ana yawan yabawa 'yan fim maganganu cewa ba sa zuwa makaranta, ba su da ilimi musamman na addini ballantana na boko.

"Da na ji ta ce ba ta damu da kallon fim ba saboda tana zuwa makaranta sai na samu karsashin nunawa masu yi mana irin wancan kallo cewa 'bari na tambaye ta kan addini domin ta nuna musu cewa ba duka aka taru aka zama daya ba'.
"Kuma ina ganin fahimta ce mutane ba su yi ba shi ya sa suke ganin kamar ba ta amsa tambayar da na yi mata ba", in ji jarumin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: