Friday, 8 December 2017
Zuwan shugaba Muhammadu buhari kano Lokaci Alkali ne

Home Zuwan shugaba Muhammadu buhari kano Lokaci Alkali ne
Ku Tura A Social Media

Zuwan Buhari Kano: Lokaci Alkali ne -Daga Yasir Ramadan Gwale
Ko mutane su yarda ko kada su yarda, Kwankwaso yana da karfi da tasiri a siyasar APC a jihar Kano. Taron jiya na taren Buhari bai yi jama’ar da muke tunani ba, sai dai fa in mutane zasu yaudari kansu.
A ganina janyewar mutanan Kwankwaso yasa aka dinga ganin wajen taron raga raga ba mutane, wani gun ma sai kaga motar Shugaban kasa ce kadai sai mutum biyu a kusa suna daga hannu. Amma kofar gidan gwamnati kan ancika.

Da ace anyi taron nan da jama’ar Kwankwaso watakila abin sai wanda ya gani. Na kuma sani mutanan da suka fito jiya, da yawansu hayarsu aka dauko a kauyukan Kano da Jigawa, kuma biyansu akai.
Koma dai meye dai kwankwaso ya nuna tafiyar APC in babu shi a Kano to tabbas akwai matsala. Ina fatan mutanan gwamnati zasu ce kai ba gaskiya bane! Ni kuma, nace lokaci alkali ne.

Ba’ko rab’a d’an gari kaba! Da fatan bakonmu ya tashi lafiya, kuma gajiya tabi jiki.
Yasir Ramadan Gwale
07-12-2017

Share this


Author: verified_user

0 Comments: