Addini

YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE ? Dr Jamilu Yusuf Zarewa

 
Tambaya? 
 
Assalamu alaykum. Tambaya  malam saurayi da budurwane shaidan yashiga tsakaninsu har yakaiga saurayin ya tsotsi qirjin budirwan har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru ba so dayaba ba biyu ba amma bata taba ganin ruwanba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu, ya halatta suyi auren? 
 
Kuma minene hukuncin shan Ruwan da yayi 
 
Amsa:
Wa’alaykumussalam, 
 
To dan’uwa wannan abin da suka aikata mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taba jikin matar da ba ka aura ba,  kuma kofa ce da za ta kai zuwa  zina, idan mutum ya tsotsi nonan mace bayan ya girma Amma babu ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma idan akwai ruwa a ciki, to
malamai sun yi sabani akan hakan
zuwa maganganu guda biyu :
 
1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure
shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru
biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha
saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102,
ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga
nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan
ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba
zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita
ce maganar mafi yawan malamai.
 
2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare
shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci matar Abu-
huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a
gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a
hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a
lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake
nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi
tasiri wajan haramcin aure.                 Zancen da ya fi karfi
shi ne nonon da mutum ya sha bayan ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba shi.
            
Don neman Karin
bayani duba : Bidayatul-mujtahid 267.
 
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saba masa zai same shi a madakata.
 
                
Allah ne mafi sani.
 
26/12/2016 
 
*Dr Jamilu zarewa*
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button