Thursday, 28 December 2017
TO FAH :- UMAR IBN KHADDAB (R.A) KARE NE :- INJI ABDULJABBAR Nasiru Kabara

Home TO FAH :- UMAR IBN KHADDAB (R.A) KARE NE :- INJI ABDULJABBAR Nasiru Kabara
Ku Tura A Social Media.
Kamar yanda daya daga cikin magabata ke cewa"Mu'awiya ibn Abu sufyan r.a kamar kyallen kofa ne duk wanda ya fara ta6a shi da sannu zai shiga zuwa ga ta6a manyan sahabbai" Hakane domin a lokacin da Abduljabbar Nasiru kabara ya fara ta6a mutuncin sahabi mu'awiya r.a malamai da dama suna cewa wallahi wannan mutumin shi'a ce yake dabaqawa ta karkashin kasa, sai ya sake fitowa da wata yaudara ta cewa wai yana kariyar ahlul baiti. Cikin wannan rigar ta ahlul baiti yake la6ewa yaci zarafin sahabbai, magabata da malamai. Amma yanzu zani rinka sawo muryarsa kowa yaji da kunnensa shi ya fada ba kage muka yi masa ba. Babbar matsalar Abduljabberi shine yiwa Annabi s.a.w tare da canza abinda ya fada kamar yanda zan kawo yanzu inda yake cewa sahabi umar r.a kare(dog) kuma har yake jaddada cewa annabi yace masa haka.kamar yanda zaku gani.
.
Abin mamaki da takaici shine akwai wani hadisi da mafi yawan yara masu karatu a islamiyya sun fahimce sosai, wannan hadisin shine"Annabi s.a.w yana mai komawa kyautarsa bayan ya bashe ta tamkar kare ne wanda idan yayi amai zai koma ya lashe shi" to amma shi Abduljebberi ba wannan ruwayar ya kawo ba. Ya kawo wace ta zo a cikin littafen bukhari hadisi na 2623.
حدثنا يحي بن قزعة:حدثنا مالك،عن زيد بن أسلم،عن أبيه:سمعت عمر بن الخطاب رضى الله عنه يقول:حملت على فرس في سبيل الله،فأضاعه الذي كان عنده، فأردت أن أشتريه منه،وظننت أنه بائعه برخص،فسألت عن ذلك النبى صلى الله عليه وسلم فقال،"لا تشتره وإن أعطاكه بدرهم واحد، فإن العائد في صدقيه كالكلب يعود في قيئه.
FASSARA:
Daga Yahaya ibn qaza'ata, daga Malik daga Zayd ibn As-lam daga babansa yace naji umar ibn khadab r.a yana cewa"na bada doki saboda Allah, sai naga wanda ni baiwa shi ya walakanta shi, sai nayi niyyar na saye shi daga garesa, kuma sai nayi zato zai ma saida mani shi da sauki(arha). Sai na tambayi annabi s.a.w shin ko zan iya sayensa? Sai Annabi s.a.w yace"kada ka saye shi koda ya saida maka shi darhami daya, sai annabi s.a.w yace"hakika mai komawa kyautarsa kamar kare ne dake komawa ga amansa.
.
To a wannan ba sai na tsaya sharhi ba don a duk hadisin nan ina ne Annabi s.a.w ya cewa Umar ibn khaddab r.a kare? Amma Abduljebberi cewa yayi"Annabi s.a.w ya cewa umar kare, wai harda maimatawa cewa Annabi s.a.w ya cewa umar ka zama kare subhanallah. Shin Allah bai yiwa Annabi karya ba? Bai canzawa Annabi s.a.w magana ba?  Ga hadisi "Mutawatiri"wanda sahabi  saba'in da biyar(75) ruwaito shi . Yana cewa"wanda duk ya yi mani karya‏ ‏da gan-gan ya za6i wurin zamansa cikin wuta.
من كذب علي متعمدا فليتبوء مقعده من النار‎  ‎
wannan karyar da gan-gan Abduljebberi ya fesa ta. cewa
العائد في صدقته كالكلب يعود في قيئه
A cikin sharhin littafen "Muwatta Malik" mai suna "Tanweerul Hawaleek" a karkashin wannan hadisi na 624 inda yake cewa
كالكلب يعود في قيئه: وجه التشبيه أنه أخرج في الصدقة أو ساخه وأدناسه فأشبه تغير الطعام إلى حال القيئ.
Misiltawa ne aka yi na dabi'ar amma ba'ana nufin mutum ba amma saboda kiyayyarsa da sahabbai ya fadi haka ga sahabi na biyu umar ibn khaddab. Allah ya karya makiya sahabbai.

Ku kasance da hausaloaded.com zamu kawo muku wannan audio inda malam abduljabar yace haka. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: