Tuesday, 12 December 2017
Ta Faru Ta ƙare: Ibn Taimiyya Ya Ce Sahabbai Ne Su Ka Fara Yin Mauludi — Sheikh Yusuf Ali

Home Ta Faru Ta ƙare: Ibn Taimiyya Ya Ce Sahabbai Ne Su Ka Fara Yin Mauludi — Sheikh Yusuf Ali
Ku Tura A Social Media
SHEIKH (DR) YUSUF ALI mashahurin malamin addinin Islama ne a Nijeriya kuma wanda ya fice wajen bayar da fatawoyi a Arewacin Nijeriya.
LEADERSHIP A YAU LAHADI ta yi tattaki gidansa da ke birnin Kano, domin tattaunawa da shi kan bikin takutaha da ke gudana a halin yanzu a ko’ina a fadin duniya, don murnar zagayowar ranar haihuwar shugaban halitta Manzon Allah Muhammad Dan Abdullah (SAW). Ga yadda hirar ta kasance:

Akrimukallah, mene ne asalin Mauludi?

Asalin mauludi malamai da dama sun yi bayani. Misali, idan mu ka dauki Shehil Islam Ibn Taimiyya ya ce, asalin mauludi shi ne lokacin da sahabbai su ka yi hijira zuwa Madina sun taru a gidan Abu Ayuba Al-ansary a inda su ka ce ya kamata mu taru mu godewa Allah da ya ba mu wannan dan taliki kuma ya sa mu ka sami shiriya da shi. Su ka taru su ka godewa Allah sannan a ka yanka akuya a ka gyara a ka rarraba. Ya ce, wannan shi ne asali. Sannan a dai wani littafin nasa shi Ibn Taimiyya, Iktirab siradil mustakim, littafi na biyu shafi na 266 ya ce, mauludi ko dai a yi shi saboda murna ta zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ko kuma a yi shi don nuna kauna ga Annabi ko kuma a yi shi don nuna kwaikwayon Kiristoci da su ke nuna murnar haihuwar Annabi Isa (AS), ya ce ko ma dai da wacce niyya a ka yi shi, Allah subhanahu wata’ala zai ba wa mutum ladan soyayyar da ladan godiya ga Allah.

Abinda ya sa kullum mu ke kawo irin su Ibn Taimiyya shi ne, saboda masu sukar mauludi su na danganta kansu da shi. Haka shi ma Imamu Suyudi babban malamin nan da ko yanzu a jami’ar Musulunci da ke Madina littafinsa, Mukararir, a ke amfani da shi wajen tafsir kuma shi ne mai littafin Tafsir jalalain a littafinsa Husnil maksad fi amalil maulud ya kira littafin da kyakkyawar manufa ta wajen yin mauludi inda ya ce, in dai mauludi za a taru a karanto sira wato tarihi na manzon Allah (SAW) A yi wadansu wakoki ko wasu kasidu ko takardu ko lakcoci da ke kunshe da nuna falala ta manzon Allah (SAW) da suke yin nuni a yi koyi da halayensa da kuma nuni da a ci gaba a gode masa saboda alherin da ya kawo ya fitar da duniya daga cikin duhu zuwa haske in dai wannan za a yi tare da yan ciye-ciye da lashe-lashe a watse to wannan abu ne kyakkyawa ko ma a ce mustahabbi.
A hadisin da Baihaki ya ruwaito ya ce, “ni na samo asalin mauludi lokacin da Annabi (SAW) ya girma ranar haihuwarsa ranar litinin cikin wannan wata ya yanka rago kuma an rarraba kyauta ga jama’a aka tambaye shi sai yace “na yi wannan yau saboda ranar haihuwa ta ce, na yi saboda na godewa Allah subhanahu wata’ala.” Annabi (SAW) ya yi wannan ne don ya assasa maulidi. Don ya yi murna da ranar haihuwarsa har ya yi yanka. Wannan lokacin Annabi bai zo Madina ba.

A wani asalin kuma imamu Bukhari da Muslim sun fitar da hadisi na Ashura a lokacin da Annabi ya zo madina sai ya samu Yahudawa suna yin biki da gangami da ado da iyalansu suna yin abinci da abubuwa na nishadi a wannan ranar sai ya yi mamaki sai suka gaya masa ai yau rana ce da Allah subhanahu wata’ala ya tserar da Annabi musa shi da Banu Isra’ila sannan ya halakar da Fir’auna shi da mutanensa don haka duk lokacin da irin wannan ranar in ta zo sukan yi irin wannan taro saboda murna. Nan sai Annabi Muhammad (SAW) ya ce, “Ai mu ne ya fi cancanta mu yi wannan saboda haka duk watan almuharram goma ga shi ake yin azimi da cika ciki. Imamu Suyudi yake cewa Lallai wanan asali ne na maulidi ya halatta in Allah ya yi maka wata falala ka gode masa in ranar ta zagayo ka gode masa in shekarar ta kuma zagayowa ka gode masa kai ta yi wanna asali ne ga shi a Bukhari da Muslim.

Babu wani malami a duniya irin wadanda su ka kai addinin Musulunci inda ya ke sai ka samu cewa ya yi wallafa a kan yabon mauludin Annabi Muhammad (SAW). Misali idan ka dauki shugaban makarantan duk duniya Imamu Jazzari Muhammad bin Muhammad bin Muhammad Aljazzari za ka samu cewa ya wallafi littafi akan mauludi har ya yi wadansu baitoci na yabon haihuwar Annabi Muhammad (SAW) Yake cewa, idan ya kasance Abu Lahab zagin sa da yi masa zambo da a ke karantawa a Tabbat yada amma kuma labari ya zo kamar yadda Bukhari ya kawo duk ranar litinin sai Allah ya saukaka masa azaba ya bubbugar da ruwa da madara a ‘yan yatsotsinsa ya sha kuma sai an dauke masa azabar wannan ranar. To ina kuma ga a ce wannan mumuni ne ya rayu akan addinin muslunci yana son Allah yana son manzonsa ya rayu a kan al’amuran muslunci har iya tsahon rayuwarsa yana kadaita Allah bai shirka ba to in a kuma ga mumini masoyin manzon Allah kai kasan ba wani sakamako da Allah zai yi masa illa kawai Aljanna. Ibn Dahiyya Alkalbi shi ma ya wallafi littafi kan falalar Mauludi. Ibn Hajar Alkassalani shi ma ya yi wallafa kan maulidi.

Ni a sanina babu wani malami kuma malamin na duniya da ya taba sukan maulidin Annabi (SAW) illa a wasu ’yan takardu da ba su wuce kwaya goma ba da ’yan jarida su ka taba yi wa Abdullahi bin Abdul’aziz Bin Baz (Allah ya gafarta ma sa) ‘interbiew’ shi ne ya taba cewa ba za a taru a nuna murna da haihuwar Annabi ba, amma fa babu aya babu hadisi ra’ayinsa; kawai ya kawo kuma duk wani da ya ke sukar mauludi wannan ya gani. Amma Ina kalubalantar wanda duk ya cika mai tsarkake sunnar Manzon Allah (SAW) da ya kawo min littafi guda daya tak da wani malami wanda ya amsa sunansa malami a duniya, kamar Turmizi, Imamu Suyidi ko Ibn Taimiyya ko Ibn Kayyim Jauziyya da makamantansu wanda su ka rubuta su ka soki mauludi, wanda wannan littafin da duk littafin da za a kawo bai wuce shekarun mai jayayyar ba ko na mahaifinsa. Haka idan an samu hujjar a Alkur’ani ko a hadisi shi ma mu na bara.

Za mu cigaba a mako mai zuwa in sha Allahu

Share this


Author: verified_user

0 Comments: