Wednesday, 6 December 2017
Shugaba Buhari Ya 'Yanta Fursunoni 500 A Kurkukun Kano

Home Shugaba Buhari Ya 'Yanta Fursunoni 500 A Kurkukun Kano
Ku Tura A Social Media

A shirin gwamnatin tarayya na rage cunkoson gidajen yari dake fadin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba ya 'yanta fursunoni guda dari biyar a gidan yarin Kurmawa dake birnin Kano.

Shugaba Buhari wanda ya je gidan yarin tare da rakiyar gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma yi kira ga wadanda aka 'yanta din da su sauya dabi'un su don ganin sun zama 'yan kasa nagari.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne shugaban kasan ya bada umarnin a rage yawan jama'ar da suke tare a gidajen yarin kasar nan sakamakon cunkushewa da gidajen yarin kasar nan suka yi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: