Sunday, 3 December 2017
Shirin Fim mai Suna " Juyin Sarauta" Na Balaraba Ramat Ya Samu Lambar Yabo

Home Shirin Fim mai Suna " Juyin Sarauta" Na Balaraba Ramat Ya Samu Lambar Yabo
Ku Tura A Social Media


Daga Haruna Akarada, Kano
A karshen satin da ya gabata ne a ka yi taron nuna fim din Juyin Sarauta wanda fitacciyar Marubuciya kuma furodusa Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ta shirya a karkashin kamfanin ta Dogarai Women Films tare da hadin gwiwa da Project Act.

Taron nuna fim din wanda aka yi a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba a dakin taro na Senior Staff Recreation Club a titin Dakta Mansur Mukhtar dake Kano ya samu halartar manyan Malamai a fannin adabi da aikin jarida da manazarta.

Da yake jawabi a game da dalilin shirya wannan taro, babban jarumin fim din Malam Ado Ahmad Gidan Dabino M.O.N, ya ce “Manufar wannan taro shi ne za a nuna wani bangare na wannan fim din mai suna Juyin Sarauta domin a bamu shawarwari da kuma gyaran da za a mu yi a fim din domin wannan za a gani wani yanki ne na fim din don shi fim din tsawon sa’o’i biyu ne amma za mu nua na minti arba’in ne domin a ba mu shawarwari da gyara. Don haka ne muka gayyato malmai da kuma manazarta domin su kalla su ga yadda abin da fim din y kunsa.”

Ya ci gaba da cewa, “Shi dai fim din Juyin Sarauta yana dauke da labarin Sarauta a kasar Hausa da kuma irin rawar da mata suke takawa a cikin gidajen Sarauta. Muna fatan za mu yi taro cikin nasara kuma muna yi wa kowa barka da zuwa.”

bayan ya gama jawabin ne sai aka fara kallon fim da misalin 12 na na inda kuma aka gama karfe biyu saura. Kuma jama’a da dama sun yaba da fim din wajen yadda ya fito da al’adun Hausa, musamman ta bangaren sarautar. Jama’a dai da dama ne suka halarci wannan kallon fim din, cikin wadanda suka halarta akwai shugaban majalisar malamai ta Jihar Kano. Malami a tsangayar aikin jarida Dakta Bala Muhammad da sauransu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: