Tuesday, 12 December 2017
Sallah! Sallah!! Sallah!!! Itace Babban Ginshiki A Musulunci karanta kuji Daga Shiekh Jabir Sani Maihula

Home Sallah! Sallah!! Sallah!!! Itace Babban Ginshiki A Musulunci karanta kuji Daga Shiekh Jabir Sani Maihula
Ku Tura A Social Media

1-Sallah itace babban ginshiki a Musulunci bayan Shahadatayn. Itace abu nafarko da za'a fara tambayar bawa a ranar qiyama, idan ta cika sauran ayukkan sun cika. Idan ta baci, ya tabe yayi hasara. Itace banbanci tsakanin Musulmi da kafiri.

2- Nigeria tana daga cikin inda akafi ko ina tsayar da sallah da kula da ita a duniya. Wataran Sheikh Abdallah Murad, wani dalibin Albany yana koyarda mu "Naylul Autar" a Jami'ar Madinah yake cewa: Naje wurare da yawa a duniya, amma ban taba ganin inda ake kula da sallah ba kamar Nigeria (Ko wata kalima kamar haka). Duk wanda yake yawo a duniya yasan maganar Sheikh gaskiya ce.

3- Cikin abinda ya burgeni na labaran kula da sallah ga 'yan Nigeria shine: satin da ya  shige wani dan Nigeria ya kirani daga London yake cewa unguwar da yake a London ba'a buda masallaci a weekends kuma jama'a basa fitowa sallar asubah saboda haka yana so ya canja unguwa. Don Allah yana so ingaya masa unguwar da ya kamata ya koma domin samun sallah. Nagaya masa cewa na taba zama da wani saurayi dan Sokoto a wata unguwa a London a 2012 yana zaune wani gida kusa da masallaci. Gidan baiyi masa ba, amma saboda kasantuwar gidan kusa da masallaci ya zauna gidan saboda son sallah. Irin wadannan misallai sunada yawa.

4- Amma fa akwai babban kalubale dake fuskantowa. Duk da cewa Masallatai suna cika da samari da dattijawa koda yaushe, amma akwai karancin yara 'yan shekara 15 zuwa kasa a masallatai. Wadannan yaran sune manyan gobe. Idan basu saba da sallah yanzu ba duk wannan falalar da muke da ita ta sallah yanzu zata tafi a gaba.

5- Mu tuna duk wannan falalar tsayar da sallah a wannan kasar tana komawa ne zuwa ga iyaye da kakanni, su sukayi mana tarbiyya suka azamu a wannan hanyar. Kada mu bari bakin wuta ya mutu a hannun mu. Mutabbata mun hori yaran mu da kannan mu da tsaida sallah. Annabi S.A.W yanacewa, "Ku umurci yaran ku da sallah suna shekara bakwai ku dakesu akan sallah da shekara goma." 

Ko wannen mu ya tabba ta ya hore dansa da 'yar sa da kanin sa da yin sallah.
Allah ya bamu ikon tsaida sallah da yinta yadda ya kamata kuma ya karba mana.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: