Uncategorized

NASIHOHI 35 Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

1- ka fara yininka da sallar asubahi da azkar domin samun rabo da tsira.

2- ka zarce da istgfari har sai shaidan ya debe
tsammanin samun rabo a jikinka.

3-kar ka daina addu’a dumin itace igiyar tsira

4-ka tuna cewa mala’iku suna rubuta maganganunka.

5-kyawun yatsu shine ka rika qidaya TASBIH dasu.

6- idan ka shiga damuwa da qunci kace” la ila ha illallah”.

7- ka sayi addu’ar talakawa da soyayyan marayu da kudadenka.

8-doguwar sujada 1 wanda aka yita saboda tsoron ALLAH yafi maka bene da aka gina na zinari.

9- ka tauna magana kafin kafadeta domin tana iya zama ajalinka.

10- ka guji addu’ar wanda aka zalunta da hawayen wanda aka hana.

11- kafin ka karanta jaridu da mujallu mai zai hana.kafara karanta alqur’ani.

12- ka zama dalilin gyaruwan iyalanka.

13- ka tilastawa ranka wurin bin dokokin Allah ,
domin ita rai tana umarni ne da sabon Allah.

14- kafin tsufar iyayanka ka daure ka samu yardarsu.

15-tsoffin tufafinka sababbi ne a wurin talakawa.

16- kar kayi fushi , domin rayuwa kadan ce ba kamar yadda kake tsammani ba.

17- tare dakai akwai wanda yafi kowa qarfi yafi kowa wadata, shine Allah.

18- kar ka rufe qofar tuba saboda sabon Allah.
19- sallah itace mafi alkhairin abun da zata taimakeka akan musibu da wahalhalu.

20- ka nisanci munanan zato, zaka huta kuma zaka hutar.

21- dalilin kowane damuwa juyawa Allah bayane, ka juyo zuwa gareshi mana.

22-kayi sallah irin wacce kakeso a shigar dakai qabari tare da ita.

23- idan kaji wanda yake gulma , kace dashi: yaji tsoron Allah.

24-ka dawwamar da kanka wurin karanta suratul MULK domin tana tseratarwa.

25- wanda aka hana( yayi hasara) shine wanda aka hanawa sallar dake cike da tsoron Allah , da idon dake zubar da hawaye.

26- kar ka cutar da bayin Allah nagari wadanda suka shagaltu da bautar Allah.

27- ka sanya soyayyar ka duka zuwa ga Allah da manzonsa.

28- ka yafewa wanda yayi gulmarka, domin ya baka kyautar kyakyawan aikinsa ne.

29- Sallah da ambaton Allah da karatun alqur’ani alqawurane masu nauyi akan qirjinka.

30- duk wanda ya tuna da zafin wuta zai iya hakuri akan sabon Allah .

31- indai ana dare gari yana wayewa, to watarana sai labari tsanani zai zama sauqi.

32- ka nisanci ANCE-KACE ( jita-jita) domin kai game da ayyuka kamar dutsene.

33- kayi sallah da tsoron Allah , domin duk abun da zakayi bayan sallar bai kai sallah ba.

34- ka sanya alqur’ani daf dakai , domin karanta aya daya acikinsa yafimaka duniya da abun dake cikinta.

35- rayuwa akwai dadi, mafi dadin rayuwa shine kaganka da iimaninka.
________________________________
ALLAH Yasa Mudace!
____________________________

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button