Wednesday, 20 December 2017
Na sha sigari na yi yan mata amma ban taba shan giya ba -inji muhammadu Buhari

Home Na sha sigari na yi yan mata amma ban taba shan giya ba -inji muhammadu Buhari
Ku Tura A Social Media
DAGA HAUSA TIMES
Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya sha Sigari sannan yayi yan mata a lokacin kuruciya.

Shugaban a hirarsa da Jaridar Sun da yake bayani kan rayuwarsa da kuruciyarsa yace sai a shekarar 1977 ya daina shan taba.
Hausa Times ta ruwaito shugaban na fadin amma dai tunda yake a rayuwarsa bai taba shan giya ko kayan maye ba.

A cewarsa, “Kwarai a lokacin kuruciya ta na sha taba sigari amma dai na daina sha ina tunanin a wajajen shekarar 1977.

“Addini na ya haramta shan kayan maye saboda haka ko lokacinda nake gidan Soja na kiyaye wannan ban taba shan giya ko kayan maye ba. [Dayake a wancen lokacin] babu mai matsa maka ka sabawa addinin ka a gidan Soja, saboda haka babu wanda ya taba tilasta ni insha kayan maye kuma ni a kashin kaina ban taba sha ba domin inaso in kasance cikin shiri a koda yaushe. Kuma ana cewa idan ka fara shan giya ko kadan ne shikenan shaye-shaye zai bi ka.

“Kuma na zaci [rashin shaye shayen] zai sa nayi kwarjini na samu farin jini wajen mata su so ni amma abun sai ya sha bamban. Sai naga matan basa bi na sai kace ina tattare da wani abu da basa so. Saboda haka ina mai tabbatar maka bana shan kayan maye, Amma na sha sigari, kuma ina da yan mata; wannan kam nayi” inji Buhari

Share this


Author: verified_user

0 Comments: