Saturday, 9 December 2017
Muhimmiyar wasiyyatar Nafisat Abdullahi ga masu son koyi da ita a duniya

Home Muhimmiyar wasiyyatar Nafisat Abdullahi ga masu son koyi da ita a duniya
Ku Tura A Social Media

Gogaggiyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta yi nasiha ga masoyan ta mata musamman ma masu so su yi koyi da ita a ruwar duniya ganin yadda ta samu nasarori da dama a harkar fim tare da lashe kambun kyaututtuka da dama.

Jarumar dai tayi wannan nasihar ne ga dumbin masoyan nata ne yayin da take fira da majiyar mu jim kadan bayan ta amshi kyaura jarumar-jarumai a fina-finan kasashen Afrika a wajen wani bikin karramawa da aka yi a birnin Landan a cikin watan da ya gabata.

Kannywoodscene  dai ta samu cewa da aka tambaye ta ko meye shawarar ta ga mata musamman ma masu sha'awar sana'ar fim din da kuma suke kallon ta a matsayin wata abar koyi a duniya, sai ta kada baki tace tana shawartar su da su kasance kan su kawai ba tare da kwaikwayon kalar rayuwar wasu ba.

A cewar ta, dukkan wadda ta ke so ta zama tauraruwa to dole ne ta guji kwaikwayon rayuwar wasu, ya kamata su zama masu yin irin rayuwar su ta kansu ba ta kwaikwayo ba ko karya sannan kuma su dage da yin aiki tukuru.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: