Monday, 18 December 2017
Muhimman Abubuwa 5 da ya faru a masana'antar kannywood cikin 2017

Home Muhimman Abubuwa 5 da ya faru a masana'antar kannywood cikin 2017
Ku Tura A Social Media
Ga muhimmin abubuwa 5 da ya faru a masana'antar kannywood kamar yanda Pulse hausa ta fitar.
 
Shekara 2017 shekara ce wanda masana'antar kannywood ta samu nasarori hakazalika ta gamu da abubuwan bakin ciki.
Wannan masanaántar wanda ke nishadantar da yan arewa a yau da kullum ta samu canji tare da samun jagorori masu taka rawan gani a fadin kasar domin wayar da kai tare da kwadartar da jama'a da irin basira da yan hausa fim ke dashi.

Ga muhimmin abubuwa 5 da ya faru a masana'antar kannywood kamar yanda Pulse hausa ta fitar;

1. Kaddamar da Kannywood Box office

Taron kaddamar da Kannywood Box Office

A cikn watan yuni na bana masana'antar kannywood ta kaddamar da kannywood Box office wanda zai taimaka wajen magance satar fasaha masu shirya fina-fina tare da kawo sauyi ta hanyar haska fina-finai a sinimomi.

An gudanar da gangamin taron kaddamarwa a tahir guest house kuma manyan-manyan jarumai da masu ruwa da tsaki a fannin yin fim sun ziyarci wajen taron.

Ta hanyar tsarin masu shirya fim sun samu damar yakar masu satar fasahar su tare da samun damar mayar da kudin da aka kashe wajen shiryawa ta hanyar haskawa a gidajen kallo da sinimomi.

Sakamakon wannan matakin yana misaltuwa da haska fim din Mansoor da Rariya da Kalan dangi da dai sauran su a sinimomi da gidajen kallo na tsawon lokaci kana aka fitar dasu kasuwa domin amfani masu siyan fina-finai a DVD.

2. Mutuwar tsohon dan wasan kwaikwayo Alhaji Kasim Yero

Kannywood ta samu babban rashi mutuwar babban dan wasa kuma tsohon jarumi wanda ya taka rawan gani a dandalin fim na masana'antu daban daban dake fadin kasa.

Alhaji Kasimu ya rasu ne ranar lahadi 3 ga watan satumba kuma anyi jana'izar shi a  babban masallaci dake maiduguri road nan garin Kaduna bayan sallar la'asar.

Mutuwar sa ya razanar da masana'antar kannywood da ma al'ummar arewacin Nijeriya. Jarumai da yan siyasan arewa sunyi jimamin mutuwar sa inda dimbin su sun jinjina masa bisa ga gudumawar da ya bayar wajen raya dandalin nishadantarwa a kasar.

A sakon ta'aziya da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai ya fitar ta hanyar kakakin sa Samuel Aruwan, gwamnan yace marigayi Alhaji kasimu tauraro ne mai haskawa kuma kwarewar sa ya taimaka wajen bunkasa al'adar yan arewa

3. Kyaututuka da samun kwangilar jakadanci

A cikin shekara 2017 jarumai kannywood da suka hada da Ali Nuhu da Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi da Aminu Sheriff da Ramadan Booth sun samu kyuatar ban girma daga kamfanoni masu taka ruwan gani a kasar nijeriya har ma da ta kasar waje.

A gasar City People awards Aminu Sheriff ya samu kyautar gwarzon shekara na farfajiyar kannywood yayin da ita ma Halima Atete ta zama takwaran shi a bangaren mata kuma. Shirin fim na farko wanda jaruma Rahama Sadau ta dauki nauyin shiryawa ya zama shirin fim wanda yayi fice a gasar.

Nafisa Abdullahi da Ramadan Booth suka lashe kyuatar gwarzon shekara ta mujallar african voice dake nan birnin Landan.Nafisa Abdullahi yayin da take amsar kyautar ta
Ali Nuhu ya amshi lambar yabo na karramawa daga BON Awards bisa ga gudumawar da yake baiwa masana'antar fina-finai dake fadin kasa a bikin karramawa wanda aka gabatar a garin Abeokuta wanda ya samu jagorancin Rahama sadau.

Banda kyaututuka wasu daga cikin masu ji a daka na masana'antar Kannywood sun samu kwangilar jakadanci na kusoshi daban daban.

An nada Sani Danja da Uzee Usman da Yakubu Muhammad a matsayin jakadun majalisar dinkin duniya a bangaren raya manufar zamani domin samun cigaba.

Hakazalika itama Nafisa Abdullahi ta kasance jakadiyar sannanen jaridar hausa ta Leadership a yau. Bugu da kari itama  Aisha Aliyu tsamiya da Ali Nuhu sun shiga sahun abokan aikin su inda kamfanin dake yin Cherie Noodles ta nada su a matsayin jagororin ta.

4. Mutuwar LIl Ameer

Mutuwar shahararen mawakin hausa hip hop Ameer Isa Hassan wanda aka fi sani da Lil Ameer ya girgiza zukata kuma ya sanya jama'a da dama sunyi kewar rashin sa.

matashin mawakin ya rasu ne sanadiyar hadarin da ya samu hanyar shi komawa gida daga a wata unguwa a jihar Kano.

Lil Ameer ya kan hanyar zama tauraro mai haskawa a fannin wakar hausa hip hop kafin ajalin sa ta riske shi.

Ya rasu yana da shekaru 14 a duniya.

5. Fitowar jarumai a fina-finan Nollywood

Hakkunde poster

Hakika daya daga cikin muhimmin abun da ya faru daga dandalin kannywood bana shine yawan fitowar wasu daga cikin jaruman ta a fina-finan Nollywood.

Manyan jarumai da suka fito a cikin manyan manyan fina-finan nollywood masu farin jini sun hada da Rahama Sadau da Ali Nuhu dda Yakubu Muhammed da Maryam Booth da Ibrahim Daddy tare da Hadiza Aliyu Gabon wanda wannan shine karo na farko da zata haska cikin shirin nollywood.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: