Tuesday, 19 December 2017
MU GUDU TARE MU TSIRA TARE Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home MU GUDU TARE MU TSIRA TARE Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media


Kayi Ibada akan sharudai guda biyu:✌đŸ»*
1. Yinta da Ikhlasi.
2. Ynita akan Sunnah.

*Ka nemi yarda guda biyu:✌đŸ»*
1. Yardar Allah.
2. Yardar Iyaye.

*Ka roqi abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Samun Rahamar Allah.
2. Tsira daga Azabar Allah.

*Ka kare abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Addinin ka.
2. Mutuncin ka.

*Ka yaqi abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Jahilci.
2. Talauci.

*Kaci moriyar abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Lokaci.
2. Lafiya.

*Ka yawaita tunanin abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Kwanciyar Kabari.
2. Tashin Alkiyama.

*Ka tabbatu akan abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Fadar gaskiya.
2. Rukon Amana.

*Ka rage abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Yawan cin abinci.
2. Yawan bacci.

*Ka yarda da abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Qaddara mai kyau.
2. Qaddara mara kyau.

*Ka fifita soyayya guda biyu:✌đŸ»*
1. Son Allah.
2. Son Manzon Allah.

*Ka siffantu da dabi'u guda biyu:✌đŸ»*
1. Ganin girman na sama.
2. Tausayawa na kasa.

*Ka nemi tsarin abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1. Shedanun cikin Aljanu.
2. Shedanun cikin Muatane.

*Ka sadaukar da rayuwar akan abubuwa guda biyu:✌đŸ»*
1.Neman ilimi.
2. Yin aiki da ilimi.

*Ka shige gaba a wajan abubuwa guda biyu:*✌đŸŒ
1. Aikin Alkhairi.
2. Kira ga Alkhairi.

*Ina fatan zakuyi abu biyu:*✌đŸŒ
1. Aiki da abinda saqon ya qunsa.
2. Turawa 'yan uwa domin su amfana.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: