Sunday, 31 December 2017
Miji Mai Wahalar Samu Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home Miji Mai Wahalar Samu Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media


Wani lokaci, Zaku dade da mace tsawon shekaru, amma dakun rabu zata manta da kai, wani lokacin kuma zaku zauna Dan lokaci da mace, amma sai ta rike ka azuci, har karshen rayuwa ta.
Mai yake faruwa?

Ga wasu siffofi da muke gani, sakamakon yau da gobe, suna yiwa mata tasiri idan mutumin da suka hadu dashi. Yana da su. :

1 Namiji wanda yasan kimar mace, da darajar ta,

2 Namiji da yake yabon mace da riritata da daukan ta da  MAHIMMANCI.

3 Namiji mai rikon amana wanda baya juyawa matar sa, baya, komai tsawon shekarun da suka dauka, da kowacce larura ta gamu da ita.

4,  Namiji da yake bawa mace cikakken lokaci, domin sauraronta da Jin raayinta.

5 Namiji mai kyauta.

6 Namijin da yake bawa mace hakuri kuma ya lallashe ta idan ya bata mata rai,ko ta shiga wata damuwa.

7 Namijin da ya tsaratar da mace daga wani Hadari da ta fuskanta a rayuwa.

8  Namijin da mace tasan zai iya mutuwa saboda ita.

9  Namiji mai faraa da murmushi da sakin fuska, da tafiye-tafiye da mace.


10 Namiji Mai tsafta da kwalliya, da  Lafiyar jiki musamman wajan biyar bukatar iyali.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: