Monday, 4 December 2017
Masu wa'azin zafin addini ne ke kara rura wutar ta'addanci - Inji Shugaba Buhari

Home Masu wa'azin zafin addini ne ke kara rura wutar ta'addanci - Inji Shugaba Buhari
Ku Tura A Social Media
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu 'yan ta'adda na cigaba ne da samun mabiya sakamakon irin yadda malamai ke cigaba da yin wa'azi mai abun da ya kira tsananin tsauri ga mabiyan su a dukkan fadin duniya.

Shugaban na Najeriya yayi wannan ikirarin ne yayin da yake ganawa da Sarkin kasar Jodan Sarkin Abdulla na II sannan kuma ya kira ga sauran shugabannin duniya da su kawo karshen hakan cikin lokaci.

Hausaloaded. com dai ta samu cewa yayin da yake jawabin nasa, shugaba Muhammadu Buhari daga nan ya kuma yi muhimmin kira ga sauran shugabannin kasashe musamman ma masu yawan musulmai da su tashi tsaye wajen gabin wannan mummunar dabi'a ta kaura a yankunan su.

Daga nan ne kuma sai shugaban ya kara jaddada aniyar Gwamnatin sa wajen tabbatar da kawar da ta'addanci daga ban kasa baki daya musamman ma dai daga yankin Afrika ta yamma.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: