Tuesday, 12 December 2017
Makarantar Dahiru Usman Bauchi Ta Yaye Mahaddatan Alkur'ani Mutum 898

Home Makarantar Dahiru Usman Bauchi Ta Yaye Mahaddatan Alkur'ani Mutum 898
Ku Tura A Social Media
Kimanin dalibai 898 ne a halin yanzu suka kammala haddar Al-Kur’ani mai girma a makarantun babban shehin malamin addinin Islamar nan kuma jagoran marhabar Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Buchi sannan kuma wasu 312 sauke ba ta hanyar handaccewa ba a fadin kasar nan.

 Darakta Janar din dake kula da harkokin ilimi a wata Gidauniyar ta Shehin malamin dake kuma zaman da ga Malamin mai suna Sheikh Sidi Aliyu Sise Dahiru Usman Bauchi da kuma Malam Hassan Adam ne suka bayyana hakan a yayin jawaban su daban daban lokacin da ake yaye wasu daliban a jihar Bauchi. 

NAIJ.com dai ta samu cewa Sheikh Sidi Aliyu Sise ya ce wannan adadin na daliban sun fito ne daga wasu makarantun dake a rassa daban-daban a jihohin Kebbi, Bauchi, Kano, Kwara, Kaduna , Adamawa, Sokoto, Zamfara,Gombe da kuma jihar Neja. Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya mun ruwaito maku cewa Shehin malamin yana wata rashin lafiya inda kuma aka nemi jama'ar musulmi da su taimaka masa da addu'o'i. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: