Tuesday, 5 December 2017
Lafazin Shiekh Ja'afar Mahmud Adam Kano (R) Game Da Mauludi Karanta

Home Lafazin Shiekh Ja'afar Mahmud Adam Kano (R) Game Da Mauludi Karanta
Ku Tura A Social Media

Malam yaci gaba da cewa:
.
"Shi yasa lokacin da muke musu da wadansu yan uwa kan batun MAULIDI MAULIDI MAULIDI muka ce duk abune mai sauqi da AKHADAREE da ISHIMAWEE da IZIYYAH da RISALA da ASKAREE da MUKHUTASAR, wadannan duk littattafai ne na koyon addini da mu da ku duk muna koyon addini a cikin su amma babu daya daga cikin su da ya kawo BABI KO FASALI NA MAULIDI.
.
Yanzu muna neman illa da tasa basu kawo ba, shin sun yi mantuwa ne? Sun jahilta ne? Ko ko ba addini ba ne don haka ba su kawo ba???
.
Saboda haka cikin wadannan dole ayi daya ko dai ya kasance mantuwa sukayi? ko ko ilimin su ne bai kai ba? Koko a fahimtar su shi din ba addini ba ne? Shiyasa basu kawo shi ba?"
.
Mallam har ya rasu baku kawo masa wadannan amsoshin ba, to mu har yanzu muna jira ku kawo mana, idan har kun gagara kawowa to muna kiran ku da kuji tsoron Allah ku dawo kubi karantarwar Alqur'ani da Sunnar Annabi (saw) sai ku samu hutu a rayuwar ku ta duniya da lahira.
.
YA ALLAH KA JIQAN SHEIKH JAFAR KA KAR6I SHAHADAR SHI.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: