Tuesday, 12 December 2017
Labari Da Dumi Duminsa:- Kotu Ta Ki Bayar Da Belin Maryan Sanda

Home Labari Da Dumi Duminsa:- Kotu Ta Ki Bayar Da Belin Maryan Sanda
Ku Tura A Social Media

Rahotanni sun nuna cewa an sake mayar da Matan nan wadda ta kashe mijinta, Maryam Sanda gidan kurkuku da ke garin Suleja a jihar Neja bayan kotun birnin tarayya ta  ki bayar da belinta.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mai Shari'a Yusuf Halilu ya nuna cewa ba zai bayar da belinta ba sai shaidu sun kammala wanda ya hada da mahaifiyar wadda ake zargin, Hajiya Maimuna Aliyu Sanda. Inda ya dage shari'ar zuwa ranar Alhamis mai zuwa.

Sai dai lauyan Maryan din, Joseph Daudu ya bayyanawa kotu cewa yanayin gidan kurkuku da Maryan ke zaune yana da matukar hadari ga lafiyar jaririnta dan wata shida da haihuwa. Idan ba a manta ba, an gurfanar da Maryam gaban kotu ne bisa zargin yin amfani da kwalba wajen kashe mijinta, Marigayi Bilyaminu Bello wanda dan tsohon Shugaban PDP, Alhaji bello Haliru Mohammed ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: