Wednesday, 27 December 2017
Labari Da Dumi Duminsa:- Dan Shugaba Buhari Ya Yi Hadari Da Babur

Home Labari Da Dumi Duminsa:- Dan Shugaba Buhari Ya Yi Hadari Da Babur
Ku Tura A Social Media

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da cewa a halin yanzu dan Shugaban Kasa, Yusuf Muhammad Buhari ya kwance a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi hadari da Babur a daren jiya a yankin Gwarimpa da ke Abuja.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa Yusuf ya samu kariya a hannu da kuma rauni a kansa amma ya nuna cewa yana ci gaba da samun sauki. Ya kara da cewa Shugaba Buhari da Uwargidansa na barar addu'a ga dan nasu don ya samu lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: