Friday, 8 December 2017
Labari A Cikin Hotuna :-An Karrama Shugabannin IZALA a Kasar Spain

Home Labari A Cikin Hotuna :-An Karrama Shugabannin IZALA a Kasar Spain
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar Wa'azin Musulunci ta Sautus Sunnah Europe mai rassa a kasashen Turai, ta karrama shugaban kungiyar jamaatu Izalatil bidah wa ikamatissunnah Sheikh Abdullah Bala Lau da Babban Sakataren kungiyar Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da shaidar (Certificate) na girmamawa Saboda gagarumar nasarorin da suka samu na da'awa da yada Sunnah wanda suka dauki kusan makwanni biyu suna yi a kasashen turai.

Kungiyar mai wa'azin Musulunci ta Sautussunnah Europe ta karrama Maluman ne a babban Masallacin jumu'a na Masjidul Huda dake birnin Barcelona a Kasar Spain jiya Laraba bayan kammala Muhadharah wacce manyan  Maluman suka gabatar.

Masoya daga cikin masallacin sunyi cuncirindo suna ta kabbara yayin da ake karrama malamansu.

Allah ya Kara daukaka Malaman Sunnah, ya bada Nasarar Da'awa.Share this


Author: verified_user

0 Comments: