Monday, 18 December 2017
KUNDIN TARIHI: Yadda Muka Kashe Ramat Murtala Mohammed – Dimka

Home KUNDIN TARIHI: Yadda Muka Kashe Ramat Murtala Mohammed – Dimka
Ku Tura A Social Media


( Daga Ahmed Abdullahi )
_____¥_______

Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 na daga cikin ranakun da suka canja tarihin Nijeriya saboda a wannan ranar ce aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed amma a karshe ba a samu nasarar juyin mulkin ba sai dai shi ya rasa ransa bayan da bijirarrun sojojin a karkashin jagorancin Lt. Col. B. Dimka.

A lokacin da aka kama Dimka kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya zayyana yadda suka shirya juyin mulkin da kuma yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya nuna cewa tun a watan Janairu na shekarar 1976 suka fara shirya makarkashiyar bayan ya sadu da wasu manyan mutane wanda ya hada har da Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon wanda a lokacin yake gudun hijira a London bayan an tunbuke shi daga mulki.

Dimka ya ci gaba da cewa, a lokacin ya samu hadin kan kananan hafsoshin soja bisa yadda ya tsara tun farko na kin saka duk wani babban hafsan soja cikin shirin juyin mulkin inda ya kara da cewa sun tuntubi Janar Bisalla wanda ya ba su karfin guiwar cewa duk abin da zai faru kada su janye batun kifar da mulkin inda ya nuna masu cewa yana cikin majalisar koli ta mulkin soja amma a duk lokacin da za a yi zama sai a tura shi wani aiki.

Dimka ya kara da cewa sun tsara kashe manyan hafsoshin soja bayan shi kansa Shugaban Kasa, Murtala Mohammed da Mataimakinsa, Cif Olusegun Obasonjo kuma wadannan manyan sojojin sun hada da, Janar T. Y Danjuma, Kanal Ibrahim Badamasi Babangida, Kanal Bajowa, Kanal Mohammed, Kwamandan rundunar Shiyyar Sokoto, Kanal Ibrahim Taiwo sai Kanal Jemibewon da ke rike da rundunar Ibadan sai Kanal Abdullahi da ke jagorantar rundunar shiyyar Jos.

Dimka ya fayyace yadda suka samu nasarar kashe Murtala inda ya ce a Ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 shi da wasu daga cikin bijirarrun sojojin sun yi kwantar bauna a daidai kan titin George da ke Legas inda Murtala zai bi ya wuce daga barikin ' Dodon Barracks' wanda a lokacin nan ne Fadar gwamnatin mulkin soja inda ya ce a lokacin da motar da ke dauke da Murtala ta doso inda suke labe sai Kyaftin Maliki ya ba su alamar tasowar tawagar Shugaban kasar wanda a cewar Dimka a lokacin da motar ta wuce inda yake, bai ganta saboda a lokacin yana Magana da wasu sai da aka ankarar da shi.

Dimka ya ci gaba da cewa, sun bi motar daga baya inda suka datse ta a daidai wani gidan man fetur da ke titin ' Bank Road' wanda daga nan ne, suka fara harbi kuma suka samu nasarar kashe Murtala Mohammed da dogarinsa, Lt. Akintunde Akinsehinwa da kuma direban motarsa. Dimka ya ce bayan sun kashe Murtala, ya tafi gidan rediyo ya bayar da sanarwar juyin mulki. Sai dai kuma an samu nasarar murkushe juyin mulkin inda aka yankewa Dimka shi da wasu mutane bakwai hukuncin kisa kuma aka zartar da hukuncin a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1976 kuma a lokacin har da Gwamnan jihar Benue Plateau, Joseph Gomwalk. ( hoton da ke kasa, a lokacin da za a zartar da hukuncin kisa ne ga Dimka da mukarrabansa a kurkukun Kirkiri)

Allah Ya Jikan Murtala Ya yi masa rahama.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: