Friday, 22 December 2017
Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan 'yan fim

Home Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan 'yan fim
Ku Tura A Social Media
Fina-finai a Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen hada kan 'yan kasa tare kuma da tabbatar da raya al'adun al'ummar mu inji Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Lamido na biyu.

Sarkin na Kano dai yayi wannan bayanin ne a yayin da wasu fitattun 'yan fim din daga masana'antar shirya fim din Hausa na Kannywood da kuma na fina-finan 'yan kudancin Najeriya watau Nollywood suka kai masa ziyara a fadar sa.

NAIJ.com dai ta samu haka zalika cewa Sarki Sanusi ya kuma bayyana cewar ko shakka babu haduwar jaruman fina-finan daga masana'antun kudu da Arewa da cewar abu ne mai kyau da zai dada kara hadin kan al'ummar kasar musamman ma a yanzu da siyasa ta raba kawunan mutane da dama.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: