Sunday, 3 December 2017
Kannywood :- Sharhin Fim Din "Gida Da Waje"

Home Kannywood :- Sharhin Fim Din "Gida Da Waje"
Ku Tura A Social Media
Tare Da: Saddika Habib Abba 09097438402 habibsaddika@gmail.com

Suna: Gida Da Waje

Tsara labari: Auwal M Sarki

furodusa: Muhammadu Mia

Bada umarni: Sadik N Mafia

Kamfani: Mia Enterprises

Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Aminu Sharif Momo, Basma Baba Hasin, Sadiya Adam, Baba Karami, Sarki Mukhtar, Sha’awa Adam, Alasan Kwalli da sauransu.

Fim din Gida da Waje labari ne akan wasu ma’aurata Faruk (Ali Nuhu) da Ramlat (Hadiza Gabon) da a ka nuna ba sa jituwa saboda halayyarsu da ba ta zo daya ba domin shi Faruk an nuna mutum ne mai son zuciya mai handama da baba ke re da kudin talakawa a kujerar sa da ya ke ta darakta mai lura da horo da kuma dibar sabbin ma’aikata na hukumar ilimin gaba da primary,  sabanin ita matar ta sa wadda kullum ta ke nuna masa cewar abinda yake yi ba dai dai ba ne shi ne dalilin daya ke san ya musu rashin jituwa.

Wannan kujerar ta Faruk da yake yin abinda ya ga da ma na handimar kudin gwamnati tare suke yi shi da wani  abokinsa Buhari (Aminu Sharif) a na cikin haka sai wani aminin Faruk (Alasan Kwalli) yaci kujerar gwamna alakarsu da faruk ta san ya ya dauki kujerar kwamishinan ilimi ya ba shi Faruk bai fa sa halinsa ba anan ma yakara samun damar handamar kudin gwamnati ana haka sai kwamitin  bincike ta kawo masa takarda akan za ta bincike shi hankalin Faruk ya yi matukar ta shi saboda ya san ba shida gaskiya bayan sun bincike shi suka tabbatar da ya ci kudin gwamnati har naira milyan casa’in da takwas na asusu sannan an sa me shi da badakala ta aringizon dibar ma’ikatan bo gi tare da karbar kudade ba bisa ka’ida ba kwamitin suka  umarce shi akan  ya dawo da kudin ko kuma su mika shi kotu.

A nan Faruk ya fara cuku cukun yanda zai ga mai girma gwanma amma abu ya gagara ko wayarsa gwamna ya ki amsawa,  Faruk yana ta fadi ta shi har Allah yasa ya sami ganin gwamna dakyar,  amma duk da haka abinda yakeso bai samu ba don gwamna sai ya nuna masa shi sam gwamnatinsa ba ta cin dukiyar al’umma ba ce saboda haka ko ya dawo da kudin da ake tuhumarsa ko kuma a mika shi kotu, Faruk ya yi kokarin su sami sa sanci shi da abokinsa mai girma gwamna amma abu bai yu ba.

Har sai da kai ya rasa aikinsa kuma an saka  masa farar takarda wadda za ta hana shi yin kowanne irin aiki a karkashin gwamnati sannan hukumar ta kwa ce gidansa da fila yensa da motocinsa amma duk da haka sai da aka biyo shi wasu ragowar kudin sakamakon babban aikin da matarsa ta ke yi a matsayinta na manaja a wani babban kamfani ya san ya ta biya wa Faruk wannan ragowar Kudaden sannan ta sai musu gidan da suke ciki a hannun hukumar hakan ta san ya basu bar gidanna su ba suka ci gaba da zama a matsayin mallakinsu.

Wannan dalilin ne ya sa ka Faruk ya koma yin zaman banza na rashin aikin yi dukkan dawainiyarsa data mahaifiyarsa data ‘yarsa Kairat (Basma Baba Hasin)  gabaki daya ta koma kan matarsa ita take komai a gidan wannan ma yakara saka musu rashin jituwa a gidan, ana cikin haka wani abokin Faruk ya samar masa aikin masinja a wani kamfani ashe kamfanin da matarsa ta ke aiki ne kuma akayi arashi aka kaishi office din matarsa domin ya zama masinjanta anan Ramla ta yi amfani da wannan  damar ta dinga hora Faruk tana ra ma abinda ya ke yima ta a gida suna ta takun sa ka har tai ga a karshe sun sami masalaha saboda barazanar takardar saki da ya yi mata Ramlat taji tsoro saboda kaunar da take yiwa mijinna ta ta dai na duk abinda take yi   har ta samar masa Babban office na P.R.O a karkashin kamafin na su.Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya fito da darasi wanda al’umma za su amfana da shi musamman ma’aikatan gwamnati.

2- Kayan aikin da aka yi amfani da su wurin guda nar da fim din sun kayatar da ma su kallo sosai musamman camera ta daukar hoto da kuma abin daukar  sauti.

3- Jaruman fim din sun yi kokari wurin isar da sakon musamman Faruk da Ramlat

4- Guraren da’aka yi amfani dasu gurin daukar shirin  sun yi kyau sun kayatar da ma su kallo musamman gida je.Kurakurai:

1- Akwai in da gwamna ya ke cewa ko ubansa ne Ayuba ya sa ci kudin al’u

Share this


Author: verified_user

0 Comments: