Tuesday, 19 December 2017
KA SHIGA TAITAYIN KA - Gargadin Rundunar 'Yansanda Ga BOSHO

Home KA SHIGA TAITAYIN KA - Gargadin Rundunar 'Yansanda Ga BOSHO
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Rabiu Kurnaa

Rundunar yansandan jihar kano ta bakin kakakinta, Dsp Magaji Musa Majia ya bayyana cewa rundunar su tana jan kunne ga dan wasan barkwancin nan, Sulaiman Bosho da ya kauracewa yin amfani da kakin yansanda a fina finan da yake futowa yana aikata laifuka irin wanda rundunar take yaki da su wanda hakan kai tsaye bata aikin hukumar ne.

Dsp Majia yace sam ba zasu lamunci wannan bata suna ba domin rundunar yansandan nigeria guda daya ce bata rabu gida gida ba, kuma an kafata ne domin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma amma bata sigar da shi Sulaiman Bosho yake amfani da kakin ba, kuma aka sarin fina finan sa kusan a haka yake fitowa matukar zai taka role a matsayin dansanda.

Ya kara da cewa rundunar su zata tuntubi shugaban hukumar tace fina finai ta jihar kano, Isma'il Afakallah akan ko yana da masaniya akan irin wannan fina finai da ake shiryawa a hukumar tasu wanda kai tsaye batanci ne ga aikin yansanda.

Daga karshe Dsp Majia, yace rundunar su a shirye take wajen basu kayan aiki da duk suke bukata wanda ya hadar da ofisoshi da bindugu marasa harsashi da sauransu a yayinda da suke shirya fina finai akan yansanda musamman wanda zai kara futo da martabar yansanda da irin kokarin da suke na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Me zakuce akan wannan gargadin?

Ibrahim Rabiu Kurna
S/A Social Media To Dsp Majia.
19-12-2017

Share this


Author: verified_user

0 Comments: