Sunday, 3 December 2017
Jarumi Adam A. Zango zai fara gabatar da wani sabon shiri Mai Suna "Karshen Zance"

Home Jarumi Adam A. Zango zai fara gabatar da wani sabon shiri Mai Suna "Karshen Zance"
Ku Tura A Social Media

Shahararren jarumin wasan Hausa, Adam A Zango, ya sanar da fara gabatar da wani shiri mai taken KARSHEN ZANCE a wannan watan da muke ciki.

Zango ya bayyana hakan ta kafar sada zumuntar Facebook a yau Lahadi. Sanarwar ta ce za a fara gabatar da shirin ne 18 ga wata.

Kamfanin RITETIME MULTIMEDIA LIMITED ne suka dauki nauyin shirin, sannan Sheikh Isa Jalo ne Darektan shirin, Nasir Gwangwazo ya rubuta, Hanan kuma ta tsara shi.
Tauraruwar Jarumi Zango na cigaba da haskawa a kamfanin shirya fina-finai na Kannywood duk da kasancewar yanzu baya shirya fina-finai a jihar Kano tun bayan samun sabani da shugaban hukumar tace fina-finai a jihar, Babannan Rabo Muhammad, shekaru da dama da suka wuce.

Tuni jarumin ya dawo jihar sa ta haihuwa, Kaduna, inda ya cigaba da sana'ar sa ta shiryawa da fitowa cikin wasan kwaikwayon Hausa.

Bayan shirin fim, jarumin kan rera wakokin zamani kala-kala.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: