Friday, 22 December 2017
Jarumi Adam A Zango Ya Bayyana Kudin da Ya kashe a Fim dinsa Na " Gwaska Return"

Home Jarumi Adam A Zango Ya Bayyana Kudin da Ya kashe a Fim dinsa Na " Gwaska Return"
Ku Tura A Social Media
Na kashe miliyan 12 kan fim din gwaska - Inji Adam A. Zango

Fim din Gwaska action fim ne, wanda akwai fada da wasan tashi a cikinsa, irin fina-finan nan ne da ake kira super-hero films, wato jarumi mai ceto al'umma

A hirarsa da 'yan jarida, Adamu Zango, ya ce, sai da fim din Gwaska ya lashe masa miliyan 12, kuma a hakan bai ma gama kashewa ba tukun.

Fim din Gwaska action fim ne, wanda akwai fada da wasan tashi a cikinsa, irin fina-finan nan ne da ake kira super-hero films, wato jarumi mai ceto al'umma, fim din zai fito a badi a watan maris.

Za'a fara bude fim din a silima da ma a wuraren da ake tsammani kamar manyan shaguna, kuma a cewar masu shirin fim din, abun ya kayatar.

An dai ga jarumai da yawa, a wurin, an kuma ga tsohuwar masoyiyarsa wato Nafisata Abdullahi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: