Wednesday, 13 December 2017
Jarumai Shida (6) Da suka Samu Nasarori da Tasiri A Masana'antar Kannywood A Cikin 2017

Home Jarumai Shida (6) Da suka Samu Nasarori da Tasiri A Masana'antar Kannywood A Cikin 2017
Ku Tura A Social Media
Yayin da shekara 2017 ke neman karewa, ga jerin jarumai biyar na masanaántar Kannywood da suka samu tasiri cikin shekarar.

Pulse ta fitar da wannan sunaye bisa ga hanyoyi daban daban wajen tantance su cikin hanyoyin akwai nuna basira da gwaninta tare da nasara da aka samu a gidajen kallon fim (sinima) da yanayin yadda ki'imar jarumin ya samu daukaka a masana'antar shirya fina fina na kasar baki daya.
Ga jaruman kamar haka;

1. Ali Nuhu

Sarkin Kannywood kamar yadda ake masa lakabi ya cigaba da nuna basirar sa » a farfajiyar shirya fina finai imma masana'antar kannywood ko ta Nollywood duk ya samu damar haskawa bana.

Fitaccen dan wasan ya shirya tare da bada umarni a shirin ''Mansoor'' wanda ya samu tarbuwa a wajen dimbin masu bibiyar fina-finai hausa.

Banda haka jarumin ya haska a fina-finan nollywood kamar ''Hakkunde" wanda ita ma jaruma Rahma Sadau ta fito a ciki, ''Banana Island Ghost'' da ''Ojukokoro".

2. Maryam Yahaya

Sabuwar jaruma Maryam Yahaya » ta shigo dandalin kannywood da kafar hagu domin tun fitowar ta a cikin shirin "Mansoor" ta fito a fina-finai daban daban bisa ga yanayin yadda ta nuna gwaninta.

Jarumar zata kara haska cikin wata sabon shiri tare da abokin aikin ta na ''Mansoor" watau
Umar M. Shereef a cikin shirin "Mariya" wanda zai fito kasuwa nan bada jimawa kuma wanda kamfanin Maishadda ta dauki nauyin shiryawa.

3. Rahama Sadau

Hakika jaruma Rahama Sadau ta taka rawan gani a harkar fim bana domin yan Nijeriya dama sun yaba kwarewarta yayin da ta fito a cikin shirin
"Hakkunde" , ''Tatu" , "Accidental Spy" , "Ajuwaya" da "Sons of the Caliphate" na masana'antar nollywood.

Shirin fim na farko da jarumar ta dauki nauyin shiryawa da kanta "Rariya" ya samu kyauta na zama shirin fim » wanda yayi fice daga masana'antar Kannywood na mujallar city people.

4. Maryam Booth

Bana Jaruma Maryam Booth ta haska a fina-finai daban daban na kannywood da nollywood masu kayatarwa. Ta fito cikin shirin "Hakkunde" da
"Rariya" har ma a cikin ''Sons of the caliphate"

5. Aminu Sheriff Momo

Bana dai shekara ce wanda tauraron jarumi Aminu Sheriff ke haskawa ganin yanda ya taka muhimiyar rawa a dandalin nishadantarwa ta kannywood. Banda fim jarumin yana gabatar shirye-shirye mabambanta masu kayatarwa a gidan telibijin ta Arewa24.
Mawuyaci ne a rasa ganin shi a cikin manya manyan fina finan hausa da suka fito cikin 2017.

Kwarewar sa da nuna gwanintar sa ya sanya mujallar city people ta karrama shi da kyautar gwarzon shekara » na farfajiyar kannywood bana.

6. Yakubu Muhammed

A halin yanzu dai wannan jarumin yana taka muhimmiyar rawa a cilkin shirin "sons of the Caliphate" tare da nuna gwanintar sa da basirar da Allah ya bashi.
Jarumin ya haska a fina-finai masu muhimanci ta nollywood da kannywood tare da gwanayen yan wasan fim » da kasar Nijeriya ke takama dasu.
Ya fito a cikin sabon shirin fim mai take "Kawayen Amarya'' wanda zai fito nan bada jimawa kuma wanda Sani Danja ya dauki nauyin shiryawa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: