Tuesday, 19 December 2017
Izala Tayi Gargadi kan Wasa Da Hakkokin Addini a Najeriya ..

Home Izala Tayi Gargadi kan Wasa Da Hakkokin Addini a Najeriya ..
Ku Tura A Social Media

..Kungiyar tayi Allah wadai da Nuna tsangwama Ga Firdausi akan sanya Hijabi

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jawo hankalin hukumomi zuwaga wani labari da ya yadu akan wata daliba musulma, mai suna Amasa Firdaos, wacce ta kammala karatunta na zama lauya amma aka hanata samun shaida saboda ta saka hijabi.

Sheikh Bala Lau yayi gargadin cewa addini baitaba zama ginshiki ko mizani ba a tsarin gwamnatin Naijeriya. Saboda haka, muna jawo hankalin mahukuntan kasar, malamai  da shuwagabanni da masu alhakin daukan ma'aikata ako wani sashi da sauran jaami'an kasar da sukiyaye sanya banbancin addini a matsayin mahangar duba cacanatar 'yan kasar a kowane irin lamari musamman duba da yawan addinan dake kasar.

Shugaban yaci gaba da cewa A yayinda muke kushe wannan Al'amari danuna rashin dacewar sa, a gefe guda kuma muna taya sauran 'yan Najeriya neman ayiwa wannar dalibar adalci kuma a gurfanar da duk masu hannu  a cikin wannan cin zarafi.
Muna kara jaddada kira ga hukumomi da 'yan kasar da suyi koyi da sauran kasashen duniya domin wayewarsu takai har ga kyale kowa yayi mu'amala gwargwadon yadda addininsa yatanadar batareda tsageranciba ga dokokin ubangiji" Inji shi"

A karshe Muna tunatar da hukumomi cewa lokaci yayi da za'a waiwayi karuwar rashin mutunta addini dayake aukuwa a baya bayannan a najeriya, Shige gona da iri da yunkurin tozartarda masu riko da addini Domin daukan matakin bai daya a kasar.

(C)  JIBWIS Nigeria

Share this


Author: verified_user

0 Comments: