Saturday, 23 December 2017
Duniya Ina Zaki Da Mu:-Ta Kashe Mijinta Da Kaninta Ta Hanyar Sanya Guba A Abinci

Home Duniya Ina Zaki Da Mu:-Ta Kashe Mijinta Da Kaninta Ta Hanyar Sanya Guba A Abinci
Ku Tura A Social Media


Wata amaryar da ba ta jima da yin aure ba, mai suna Dausiya Abdulmumin, da ke Unguwar Danmayaki a jihar Katsina, ta shiga hannun jami'an tsaro sakamakon kashe mijin ta mai suna Saminu Usman da kaninta Muhammad Abdulmumin da ta yi.

Rahotanni sun nuna cewa Dausiyya ta sanya guba ne a abincin mijin, wanda hakan ya zama sanadiyyar rasuwar mijin da dan uwanta da ke zaune a gidan.

Haka kuma wata kanwar mijin mai suna Sha'afatu Usman ta tsallake rijiya da baya sakamakon ceto rayuwar ta da aka yi. 

A yayin jin ta bakin kakakin rundunar 'Yansandan jihar Katsina DSP Gambo Isah game da lamarin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da bayyana cewa Dausiyya ta amsa laifin da ake zargin ta da shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: