Labarai

Dukkannin Ma’aikatan Da El Rufa’i Ya Kora Za Mu Dawo Da Su Bakin Aiki Idan Mun Kawar Da Shi A 2019, Inji Sanata Shehu SaniDaga Ibrahim Ammani Kaduna 

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar a shirye yake ya dawo da dukkanin Ma’aikatan Jihar da Gwamna Nasiru El Rufa’I ya kora daga bakin aikin su, idan Allah ya nufa sun kori El Rufa’I daga fadar Gwamnatin Jihar a shekarar zabe ta 2019, domin dawo da Jama’ar Jihar cikin hayyacin su. 

Dan Majalisar ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Ofishin Kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomin Jihar dake Kaduna, domin jajanta musu akan hatsarin da su ka tsinci kansu a ciki biyo bayan matakin da El Rufa’I ya dauka na korar Ma’aikatan kananan Hukumomin Jihar har kimanin 4300.

Sanata Shehu Sani ya cigaba da cewar ko kadan a matsayin shi na Dan Majalisa sannan Dan rajin kare hakkin Bil Adama, ba zai zauna ya zura idanuwa sannan ya rungume hannu yana kallon ana azabtar da Jama’ar Jihar kaduna ba wadanda suka fito kwan su da kwarkwatar su suka zabi Gwamnan da fatan samun kyakkyawan canji, amma sai ga shi kafin aje ko’ina Gwamnan ya sauya ya juyo da kazamin makami akan Jama’ar Jihar yana barazana ga rayuwar su, wanda wannan a fili ya nuna cewar Gwamnan ya yi hannun riga da manufar Jam’iyyar APC wacce ta kawo shi matsayin da ya ke kai. 

Dan Majalisar Dattawan wanda ya koka matuka akan irin halin da Jama’ar Jihar Kaduna su ka tsinci kansu a ciki biyo bayan abinda ya kira bakin mulki na El Rufa’I, yace a halin da ake ciki yanzu talakan Jihar Borno ya fi talakan jihar Kaduna natsuwa da kwanciyar hankali, saboda matsalar Jihar Borno matsala ce ta tsaro kawai, kuma a halin da ake ciki yanzu wannan matsala an ci karfin ta, amma Jihar Kaduna tana fama da dukkanin wadannan matsaloli tun daga fannin tsaro da annobar koran jama’a akan aiki ba gaira babu dalili, saboda haka ya zama wajibi ya jajantawa Jama’ar Jihar akan iftila’in da ya fada musu, gami da basu tabbacin komai zai daidaita a jihar idan akayi nasarar korar El Rufa’I akan karagar mulki. 

Lokacin da ya ke mayar da jawabi Sakataren Kungiyar Ma’aikatan kananan hukumomin Jihar ta Kaduna Mista Terry Henry Issac, yace suna matukar godiya da nuna goyon bayan su akan muradin Sanata Shehu Sani, sannan a hannu guda sun yi nadamar zaben El Rufa’i a matsayin Gwamna, wanda tun asali sun zabe shi ne saboda ya shiga Rigar Buhari, kuma a yayin yakin neman zabe ya yi musu alkawarin kara daukar Ma’aikata ne, amma abin mamaki maimakon a dauki Ma’aikata sai aka koma korar Ma’aikata, a bisa ga wannan dalilin suka fahimci El Rufa’I ba mai alkawari ba ne, saboda haka sun cire sunan Malam daga cikin sunan shi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?