Kannywood

Dandalin Kannywood: Ni jawara ce mai ‘ya’ya 2 amma ba na so a sani – Inji Jaruma Teema Yola

Fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood wadda ta dade tana bayar da gudummuwar ta masana’antar mai suna Fatima Isa Muhammad Yola wadda aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa tabbas ta taba aure har ma tana da ‘ya’ya biyu yanzu haka amma bata so tana yaya ta hakan saboda yanayin sana’a ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take yin fira da majiyar mu ta jaridar Blueprint inda take yin karin haske a game da rayuwar ta a baya da kuma yanzu.

Hausaloaded.com dai ta samu cewa Teema Yola ta bayyana babban dalilin da yasa bata son tana yayata zawarcin nata shine saboda kada ta kori wasu mazan dake son ta da aure.

Haka zalika jarumar ta bayyana cewa a kowane lokaci idan dai har ta samu namijin da take so zata yi auren ta domin a cewar ta cikar mace kenan a dakin mijin ta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button