Monday, 25 December 2017
Da Kyau Jarumi Zaharradeen sani Ya Tafi ƙasar Saudiyya Wajen Karu Karatu

Home Da Kyau Jarumi Zaharradeen sani Ya Tafi ƙasar Saudiyya Wajen Karu Karatu
Ku Tura A Social Media
Daya daga cikin fitattun matasan jaruman nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Zaharadeeni Sani ya sanar da cewa yanzu haka yana fadada karatun sa ne a wata makaranta dake a garin Riyad can kasar Saudiyya.

Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattaunawa da majiyar mu ta mujallar Fim game da yadda ba'a ganin sa a fina-finai da yawa a halin yanzu.

jarumin ya kuma bayyana cewa duk da hakan, yanzu haka yana nan akan shirya fim din sa mai suna 'Sangarta' a can kasar Saudiyya din.

Daga karshe sai kuma ya godewa masoyan sa da dukkan saunan masu bibiyar harkokin masana'antar ta sa sannan kuma ya sha alwashin cigaba da harkar fim din da zarar ya dawo gida Najeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: