Saturday, 2 December 2017
Budaddiyar Wasika Zuwa ga Sheikh Sani Yahaya Jingir

Home Budaddiyar Wasika Zuwa ga Sheikh Sani Yahaya Jingir
Ku Tura A Social Media


Assalamu'alaikum warah Matullahi Wa Bara Katuhu.

A madadin 'Yan kwamitin Yanar Gizo ta wannan kungiya, muna neman Alfarma a wajen Uban gayya Uban Tafiya Fadhilatus Sheikh Sani Yahaya jingir, cewa ya taimaka ya daina kiran sunan Sheikh Abdullahi Bala Lau akan mumbari yana cin mutuncin sa, tare da masa kage kala kala, lura da Sheikh Bala Lau bai taba ambatar sa yayi masa cin mutunci akan mumbari ba.

Bama jin dadi ko kadan muga yan kafafen sadarwar zamani suna ta zage zage da aibata Malaman Sunnah a facebook, kuma hakan yana faruwa ne kadai in Sheikh Sani Yahaya jingir ya aibata su Sheikh Bala Lau akan mumbarin wa'azi.

Akaramakallahu mumbarin Izala Mimbarin Wa'azi ne, a taimaka ayi wa'azi wannan shine abun da zai kawo karshen aibata Malaman sunnah a zaurukan facebook.

Yau Asabar da gobe Lahadi kungiyar Izala karkashin Sheikh Bala Lau tana wa'azi a Garin kontagora ta jihar Niger, haka zalika Izalar Jos karkashin sheikh Jingir tana wa'azi a birnin Katsina, Akaramakallahu muna neman Alfarmar Kada a aibata Su Sheikh Bala Lau, domain a dakile zage zage da Mabiya sukeyi a facebook.
Da fatan za'a fara wa'azuzzuka lafiya a kare lafiya. Kuma Allah ya sa Malam ya dauki shawarar mu. Amin

Rahoto Daga :- jibwis Nigeria

Share this


Author: verified_user

0 Comments: