Monday, 4 December 2017
Bana tunanin akwai wanda zai iya kada Ganduje a zaben 2019 – Kwankwaso

Home Bana tunanin akwai wanda zai iya kada Ganduje a zaben 2019 – Kwankwaso
Ku Tura A Social Media
Kwamishinan ayyuka na musamman, Musa Iliyasu Kwakwaso ya bayyana cewa jama’an jihar Kano zasu sake zaben gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a karo na biyu a shekarar 2019.

Kwankwaso ya danganta sake komawa kujerar gwamnan jihar Kano na Ganduje ga kyawawan ayyukan alherin daya shimfida ma al’ummar jihar Kano, sa’annan ya kara da cewa shugaba Buhari ma zai koma kujerarsa.

A yayin zantawa da Kwankwaso, Jaridar Abusidiq ta ruwaito shi yana fadin “Sanin kowa ne Kano ce ke bada kuri’u masu yawa a kowani zabe, don haka ina tabbatar muku Kano ta Buhari da Ganduje ce, kuma Ganduje na tare da nasara.”Kwankwaso ya kara da cewa ayyukan alherin da Ganduje yayi ne zai sa Kanawa su sake zabensa, musamman manyan ayyuka da suka shafi al’umma, kamar Asibitin yara dake titin gidan Zoo, da na Badawa wanda ya kammala ayyukansu.

“A yanzu haka gwamna Ganduje ya kammala ayyukan Asibitocin nan, tare da sanya musu kayan aiki na zamani, kuma ana sa ran shugaban kasa Buhari zai kaddamar da su.” Inji Kwankwaso.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: