Monday, 4 December 2017
Atiku ga Lai Mohammed: Baka isa ka hana PDP koma mulki ba

Home Atiku ga Lai Mohammed: Baka isa ka hana PDP koma mulki ba
Ku Tura A Social Media
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya gargadi yan siyasa daga furta kalamai marasa kan gado a yayin da zabukan 2019 ke karatowa, inji rahoton Premium Times.

Atiku ya bayyana haka ne yayi dayake karanta jawabinsa na ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PDP, inda yake amsa tambayar wata mai sararo da ta ce masa “Menen yasa ka koma PDP, bayan Ministan watsa labaru, Lai Muhammed ya tabbatar da cewa PDP ba zata sake komawa mulki ba?”Tsohon mataimakin shugaba Atiku yace mutum mai yawan alfahari ne kawai dinga hasashen jam’iyyar da ba zata kai labari ba tun yanzu, yace Allah ne kadai zai iya sanin wannan.


Atiku
“Babu wanda ya san abin da ke gaba, idan ba Allah ba, don haka babu mutumin daya isa yayi wannan. Kuma wannan sauyin sheka da nayi, nayi ne don Najeriya ba wai don kwadayin mulki ba.” Inji Atiku.

Majiyar Hausaloaded .com ta ruwaito rahotanni sun tabbatar da Ministan watsa labaru, Alhaji Lai Muhammed ya fadi a Jihar Jigawa cewa PDP ba zata sake komawa mulki ba, musamman ganin kokarin da gwamnatin Buhari ke yi.

Ita dai jam’iyyar PDP ita ce jam’iyyar da ta sha kayi a hannun Jam’iyyar APC, a zaben shekarar 2015 a karkashin shugaban kasa Goodluck Jonathan, bayan ta kwashe shekaru 16 tana mulkin Najeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: