Monday, 4 December 2017
Asalin Tsakani Na Da Rahama Sadau Inji Nafisa Abdullahi

Home Asalin Tsakani Na Da Rahama Sadau Inji Nafisa Abdullahi
Ku Tura A Social Media
A wani karon kuma, jaruma Nafisa Abdullahi ta fito tayi bayani dalla-dalla game da ainihin alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami.

Jarumar dai tayi wannan karin haske ne yayin wata fira da Weekly Trust jim-kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita zaune take lafiya da kowane abokin sana'ar ta.

Hausaloaded .com dai ta samu cewar da aka tambaye ta ko da gaske ne ba su ga-maciji da junan su ita da korarrar jarumar nan Rahama Sadau, sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani tsabani a tsakanin su yanzu.

Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma dukkan su suna yin aiki ne a karkashin kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace kuma suna fada da junan su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: