Friday, 22 December 2017
Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale

Home Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale
Ku Tura A Social Media
Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa yanzu haka akwai soyayya mai karfi a tsakanin fitattun jaruman nan na fina-finan Hausa watau Baballe Hayatu da kuma Sadiya Gyale.

Kishin-kishin din soyayyar ta su ma dai ya kara karfi ne bayan da wasu zafafan hotunan su suka fita a kafafen sadarwar zamani dauke da su cikin irin siga ta ma'aurata ko kuma ta masu shirin aure.Hausaloaded .com dai ta samu cewa shi Baballe Hayatu yana daya daga cikin manyan maza da suka dade suna harkar fim din amma kuma har yanzu bai taba yin aure ba watau ma'a dai shi har yanzu tazuru ne.

Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa Sadiya Gyale fitacciyar jaruma ce da ta taka muhimmiyar rawa a shekarun baya tun masana'antar fim din ma tana tasowa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: