Labarai

An Tsinci Jarirai Biyu A Jihar Kebbi Daya a Mace, Daya a raye kalla cikin Hotona

                         

Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta bada sanarwar an kawo mata rahotan jarirrai biyu da aka jefar daya matacce dayan kuma a raye.

 Alhaji Ibrahim Ahmed Gwadamgaji ya bayyana cewar dayan jaririya ce aka tsinta matatta a unguwar Gesse phase 1 bayan ofishin JNI a garin Birnin Kebbi. Sai dayan namiji ne an tsince shi a hanyar Bawada ta gundumar Gulumbe a karamar hukumar Birnin kebbi.

Ya bayyana cewar wannan mugun aiki ne da wasu marasa imani ke aikatawa, ya la’anci masu aikata wannan munmunar aikin.

A nasa bangaren, Malam Muhammad Nayilwa limamin masallacin Juma’a na Wuronori dake Birnin Kebbi, ya bayyana bacin ransa kan wannan lamarin. Inda ya yi kira ga al’umma da su ji tsoron Allah su bar aikata munmunan aiki.

Ya ce mutane su tuna cewa kowa zai yi bayanin abinda ya aikata a gaban Allah. Ya yi kira ga mutane su tuna cewa za a mutu sannan duniyar nan ba wurin zama ba ce,kowa zai mutum. Don haka yake kira ga al’umna da aikata alheri domin samun rahamar Allah.

Wani bawan Allah da bai so a fadi sunan sa ba, ya yi alkawarin bada babban goro ga duk wanda ya bada bayani da zai sa a gono wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button