Saturday, 9 December 2017
An Nada Ali Artwork Sarkin Barkwanci Na Kasar Hausa

Home An Nada Ali Artwork Sarkin Barkwanci Na Kasar Hausa
Ku Tura A Social Media
mar da cigaba ga matasan al'ummar Hausawa da Fulani watau Hausa/Fulani Youth Development and Orientation Forum (HAFYDOF) a turance ta nada fitaccen mai barkwancin nan a masana'antar Kannywood watau Aliyu Muhammad Idris a matsayin sarkin masu barkwancin kasar Hausa.

Fitaccen mai barkwancin dai da aka fi sani da Ali Art Network ya karbi kyautar ne a karshen satin da ya gabata a garin Kaduna.

Hausaloaded.com dai haka zalika ta samu cewa da yake jawabi yayin bayar da kyautar, shugaban kungiyar Alhaji Abdulaziz Muhammad Tibibi ya bayyana cewa musabbabin makasudin bayar da kyautar shine domin yabawa mai barkwancin ga irin gudummuwar da yake bayarwa ga cigaban matasa da kuma al'adar Hausa.

Shima da yake tsokaci jim kadan bayan karbar kyautar, Ali Artwork ya sha alwashin cigaba da yada manufar zaman lafiya da kuma dogaro da kai a tsakanin matasan yankin Arewa da ma su anfani da yaren Hausa a ko ina suke cikin duniya. D

Share this


Author: verified_user

0 Comments: