Saturday, 9 December 2017
An kashe ma fim din Hausa da aka Shirya akan Boko haram Naira miliyon Dari uku

Home An kashe ma fim din Hausa da aka Shirya akan Boko haram Naira miliyon Dari uku
Ku Tura A Social Media


'Make Room’ fim ne mai suna da Turanci amma aka dauke shi da harshen Hausa, sannan jaruman Kannywood kamarsu Yakubu Muhammad da Suji Jos da Sadi Sawaba da Usman Uzee da Asabe Madaki da Abba Zaky da sauransu suka taka muhimmiyar rawa a cikinsa.

Jigon labarin fim din a kan Salma (Asabe Madaki) ’yar shekara 17 ne. Salma ita kadai ce a wurin mahaifanta, kuma yarinya ce mai cike da burin yin karatun boko; yarinya ce mai jajircewa da tsayawa kai da fata wajen ganin ta cimma burinta ba tare da tunanin abin da zai je ya zo ba.

Duk burin da Salma take so ta cimma ya hadu da cikas ne a lokacin da ’yan ta’adda suka saceta hade da yin garkuwa da ita, inda ta fada cikin mawuyacin hali, sannan duniya ta yi mata daci.
Fim din ‘Make Room’ wanda kamfani Natibe Media ya dauki nauyin shirya shi, ya fito da kananan jarumai dubu uku da manya da matsakaitan jarumai 100 da kuma ma’aikatan bayan kyamara 100.

Labari ne da ke kunshe da irin yadda ’yan ta’adda suka ci karensu babu babbaka a Arewa maso Gabashin kasar nan.
An shafe fiye da kwana 50 wajen daukar fim din, inda aka dauke shi a kauyen Ijebu-Miango da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, inda aka yi hasashen kasafin kudin fim din ya kai kimanin Naira miliyan 300.

Babban Furodusan fim din, Rogers Ofime a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya ya bayyana cewa, burin da suke da shi dangane da fim din shi ne, su fafata da shi a gasar Oscar ta duniya, inda za su shiga rukuni uku da shi, wadanda suka kunshi, Gwarzon Gajeren Fim da Gwarzon Fim Ba Na Turanci Ba da kuma Gwarzuwar Jaruma, sakamakon rawar da jarumar fim din Asabe Madaki ta taka a fim din.

Ofime, wanda ya shirya manyan fina-finan Turanci irinsu ‘Oloibiri’ da ‘House of Barakat’ da kuma fitattun fina-finan Turanci da ake nunawa a gidajen talabijin irinsu ‘Tinsel’ da ‘The Johnson’ ya bayyana fim din ‘Make Room’ shi ne fim mafi wahala da ya shirya tun da ya fara harkar fim a 2001.

Ya ce, “Ba za ka taba sanin baiwa da basirarka ba sai ka samu kanka cikin wani mawuyacin halin da ba ka tunanin za ka iya fita daga cikinsa. Kafin mu kai ga daukar fim din, ina cike da burin zan shirya hadadden fim, domin ina da burin samun gudunmuwar kudi, a lokacin da muka cimma yarjejeniya da wadanda za su taimaka har rawa na yi, amma mako daya kafin mu fara daukar fim din suka janye.”

Ya ce, ya shiga cikin matsananciyar damuwa da kuma fargaba, saboda ya riga ya gayyato ma’aikata daga Amurka da Afrika ta Kudu da Najeriya da sauran wadansu kasashe.

Furodusan wanda ya lashe Gwarzon Bakon Fim a shekarar 2016 yayin Gasar Black Film Festibal da aka gudanar a San Diego, da ke Kalifoniya a Amurka, ya ce ya tambayi kansa ko ya fasa daukar fim din ne? “Sai na ce ba zan taba bari don wadanda muka yi hadaka da su sun janye in hakura ba. Domin wannan fim ne da zai yi shura a duniya.”

“Daga karshe na yanke shawarar ci gaba da daukarsa, kuma cikin ikon Allah ga shi mun kai ga karshensa.” Inji shi.
Ofime, mai kimanin shekara 44 da ya fara harkar fim da wani kamfani mai shirya fina-finai da ke Afrika ta Kudu mai suna Sky Sweeper Films a shekarar 2001, ya kara da cewa wannan fim din ya koya masa darasin komai zai yi idan zai jajirce da kuma addu’a, to zai samu nasara.

Asabe Madaki wadda ita ce babbar jarumar fim din, ta ce babban kalubale da ta samu yayin daukar fim din, shi ne ta zama Salma, domin ita ba karamar yarinya ba ce, don haka yin abu kamar yarinya ya ba ta wahala.

Jarumar wadda ita ce babbar jarumar fim din ‘Sarauniya’, ta ce fitowar da tafi ba ta wahala a fim din ita ce, fitowar da ’yan ta’adda suka yi mata duka da kuma fyade da kuma fitowar da ake nuna ta tana haihuwa.

Abba Ali Zaki wanda ya fito a matsayin Bulus a fim din, mai walda ne a garin Maiduguri, inda ya kasance maraya bayan ya rasa mahaifansa, sannan yake gudanar da sana’arsa har zuwa lokacin da ’yan ta’adda suka sace shi hade da mayar da shi dan ta’adda.

Ya bayyana cewa fitowar da ya fi so a fim din ita ce lokacin da ya yi ja-in-ja da ’yan ta’adda yayin da suke kokarin tafiya da matarsa, “Ina son wannan fitowar ne saboda jaruntar da na nuna a gaban ’yan ta’addan.”

Ya ce fitowar da ya fi shan wahala ita ce a lokacin da ’yan ta’adda suke bin sa don su kashe shi, “A lokacin ina azumi, kuma fitowar ta gudu ce, na sha wahala sosai.”

Jamila Yahaya Ibrahim, wadda ta fito a matsayin Umma a fim din, ta ce Umma wata yarinya ce da dan uwanta kadai ne ya rage mata a duniya, ta ce fim din yana dauke da darussa masu yawa.
“Fitowar da tafi ba ni wahala ita ce lokacin da na taimaka wa Salma ta haihu, ban taba samun kaina a irin wannan yanayin ba.” Inji ta.

Jamila, mai shekara 24 ta ce fim din yana koyar da muhimmancin zaman lafiya da kuma koyar da yadda za a guji tayar da zaune-tsaye.
Ta ce wuraren da aka dauki fim din sun dace da labarin, sai dai babban kalubalen da ta fuskanta shi ne ta zama ‘Umma’ a fim din.

“Dalilin ya sanya na sha wahala shi ne, ni ba Bahaushiya ba ce, ni kabilar Gbagyi ce, akwai maganganun da suka yi mini tsauri.” Inji ta.

Abubakar S Mohammed, wanda shi ne Darakta na II a fim din, ya bayyana cewa an kashe miloyin Naira a fim din.

“An kashe miliyoyin Naira wajen daukar fim din, an ciyar da mutane fiye da dubu 3 tsawon kwana fiye da 50, an biya su kudin aikinsu. Hatta gidajen da ‘yan ta’adda suka yi amfani da su ginawa muka yi, ga motocin Hilud fiye 10 da ‘yan ta’adda ke amfani da su, inda wadannan motoci hayarsu aka yi.” inji shi.

Ya kara da cewa, an gayyato kwararrun ma’aikata daga kasashen waje, kuma su ma biyansu aka yi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: