Friday, 1 December 2017
An Kaddamar Da Sabuwar Manhajar Karatu A Yanar Gizo

Home An Kaddamar Da Sabuwar Manhajar Karatu A Yanar Gizo
Ku Tura A Social Media

A jiya ne aka kaddamar da sabuwar hanyar karatu a yanar gizo mafi sauki; wato www.mylearningacadem­y.com . Wannnan manhaja dai kokari ne da wani dan Arewa na farko ya yi, wanda ba a taba samun irinsa ba a Arewacin Najeriya.

Bikin kaddamarwar ya wakana ne a hotel din Transcorp da ke Abuja, kuma taron ya sami halarta masana da jami'an tsaro da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati da wakilai daga kungiyoyi irin su UNESCO da masu ruwa da tsaki a kan sha'anin ilimi.

Babban mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin Duniya, Hajiya Amina Muhammad ta albarci taro da kuma kira ga al'umma da su yi amfani da wannan manhajar don kara ilimi.

Wannan kalubale ne ga hukumomi da ma'aikatu da kungiyoyi masu zaman kansu da su sani cewa Arewa fa akwai masu hazaka da basira.
www.mylearningacademy.com
mylearningacademy.comShare this


Author: verified_user

0 Comments: