Monday, 11 December 2017
An ci zarafin jarumar fim din Dangal Zaira Wasim a cikin Jirgi

Home An ci zarafin jarumar fim din Dangal Zaira Wasim a cikin Jirgi
Ku Tura A Social Media
'Yan sanda a Mumbai na kasar India, sun kama wani mutum da ake zargi da cin zarafin wata jaruma 'yar kimanin shekara 17 da haihuwa a lokacin da suke cikin jirgin sama.

Zaira Wasim, ta wallafa a shafinta na Instagram wanda ta ke da masu binta kusan dubu 400 cewa, wani mutum mai matsaikacin shekaru da ke zaune a bayan kujerarta a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Mumbai daga Delhi, ya rinka shafa mata wuyanta har zuwa bayanta da kafarsa a lokacin da ta ke gyangyadi.

Zaira Wasim, wadda ta fito a cikin fina-finai biyu da suka yi fice a kasar india, wato Dangal da kuma Secret Superstar, ta ce " Ina cikin gyangyadina mai dadi sai na rinka jin kamar abu yana bin bayana, da farko sai na yi watsi, to amma sai na ji har an taho ta bayana, anan ne na farga cewa lallai shafa ni ake yi ba zato nake ba".

Jarumar a shafin nata na Instagram, ta ce ta so ta dauki hoton bidiyon mutumin a lokacin da ya ke shafa mata jikin da kafarsa, amma saboda ba haske a cikin jirgin ba ta yi nasara ba.
Zaira Wasim ta ce, ta so yin hakan ne saboda shaida, to amma duk da haka ta tona masa asiri kuma yanzu haka yana hannun hukuma.

Ta ce "Idan irin haka ta samu wata, to dole ta tona asirin wanda ya aikata, saboda sai mun taimaka wa kanmu kafin wani ya taimake mu".

Yanzu haka dai kamfanin jirgin mai suna Air Vistara, ya nemi afuwar jarumar ya na mai cewa bai san hakan ya faru ba sai bayan sun isa Mumbai, kuma ba zai taba lamuntar irin wannan halayya a cikin jirginsa ba.

Rahoto daga bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: