Wednesday, 6 December 2017
An Bayyana Shugabancin Isa Ali Pantami A Matsayin Babban Cigaba Ga Harkar Tattalin Arzikin Nijeriya

Home An Bayyana Shugabancin Isa Ali Pantami A Matsayin Babban Cigaba Ga Harkar Tattalin Arzikin Nijeriya
Ku Tura A Social Media


Daga Ibrahim Baba Suleiman

An bayyana shugabancin Dr.  Isa Ali Pantami a ma'aikatar fasahar bayanai ta kasa (NITDA) a matsayin babban cigaba ga harkar fasahar bayanai da tattalin arzikin kasar Nijeriya.

Babatunde Otumala ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin nuna goyan baya da kungiyoyin kare hakkin farar hula suka gabatar a 'Unity Fountain' dake birnin tarayya Abuja.

Babatunde yace zuwan Dr. Pantami wannan fanni yayi armashi sosai musamman ga yaki da cin hanci da rashawa a ma'aikatu.

A saboda haka, Babatunde yace shugaban kasa Buhari ya chanchanchi a yaba masa bisa nadin Pantami wanda ya dace da aikin don jagorantar fannin wanda yake da damammaki sosai ga matasa da ma kasa baki daya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: