Allahu Akbar: Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa


Da safiyar yau ne dai muka samu labarin rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya mai suna Alhaji Gidado Idris yana mai shekaru 82 a duniya.

Gwamnan jihar Kaduna ne dai Malam Nasir El-Rufa'I ya fitar da sanarwar a shafin sa na dandalin sadar da zumunta na Facebook inda ya kuma bayyana cewa ya rasu ne a jiya Juma'a.

Hausaloaded .com dai ta samu cewa marigayi Gidado Idris ya riski al'amurra da dama a lokacin rayuwar sa na tarihin Najeriya shekaru da dama da kafuwar ta.

Rahotannin tarihi sun bayyana cewa shine mutumen da ya taimaka wajen gane gawar marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a lokacin da aka kashe shi a yayin juyin mulkin Inyamurai na farko karkashin jagorancin Major Kaduna Nzeogwu a shekarar 1966.

Share this


0 comments:

Post a Comment