Thursday, 2 November 2017
Wata tsaleliyar budurwar ta bayyana sha'awar ta na takarar kujeran majalisa a Bauchi 2019 Ga Manufofinta a Taƙaice

Home Wata tsaleliyar budurwar ta bayyana sha'awar ta na takarar kujeran majalisa a Bauchi 2019 Ga Manufofinta a Taƙaice
Ku Tura A Social Media

Wata budurwa ta bayyana shawarta na tsaya wa takarar kujeran sanata a jihar Bauchi

- Budurwar mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir har ma ta bayyana tsare-tsaren guda 9 da ta tanadar ma mutanen yankin ta idan har sun zabe ta

A halin yanzu da yan Najeriya ke shirye-shiryen fuskantar babban zaben shekarar 2018, matasa da dama na nuna sha'awarsu ta tsayawa takara a zaben.

Wannan ya biyo bayan kudirin rage shekaru na takara da Majalissar Najeriya ta rattafa hannu a kai kwanakin baya waddaya baiwa matasa masu kananan shekaru fitowa takarar.

Wata budurwa mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir ta bayyana sha'awar ta na tsayawa takarar kujerar Sanata a yankin Bauchi ta kudu a zaben 2019 mai zuwa.
Daga shafinta na instagram  


Bayan bayyana sha'awar nata ta shafin sada zumunta na Istagram, Ziyaatulhaqq ta zayyana abubuwan da zata yima al'ummar mazabar ta kamar haka:

Mazabar Bauchi ta Kudu ku fito ku zabi Ziyaatulhaqq Uman Tahir

1) Ilimi kyauta mun mun dauke wa iyayen ku

2) Zamu dauke wa iyayen yara mata kayan daki

3) Iyaye mata za'a ware masu albashin N100,000 duk wata ladan tarbiyar da suk wa yaran mu

4) Zamu han yan mata talle

5) Duk wanda yayi fyade za'ayi masa sabuwar kaciya sannan a daure shi gidan yari har tsawon shekaru 25


6) Zamu aurar da zaurawa da mutunci

7) Zamu tallafwa marayu har karshen rayuwarsu

8) Zamu gyara yankin Bauchi ta Kudu

9) Zamu kauda talauci da handama, rashin ilimi da babakere

Share this


Author: verified_user

0 Comments: