Wednesday, 1 November 2017
Wata Sabuwa Soyayya Ba Tabbas Ya bashi kyautar mota bayan yayi ma matarsa ciki

Home Wata Sabuwa Soyayya Ba Tabbas Ya bashi kyautar mota bayan yayi ma matarsa ciki
Ku Tura A Social Media
Wani dan Nijeriya ya bada ƙyautar mota ga wani dan ƙasar Afrika ta kudu bayan yayi wa matar sa ciki.

A bisa labarin da wana kafar yada labarai dake kasar afrika ta kudu , dan Njeriyan mai suna John yace fushin mijin ya sauka bayan ya bashi kyautar katafaren motar.

"Na san abun da na aikata ba daidai bane amma naji dadi da ya amshi kyautar da na bashi. Ya yarda cewa matar sa wanda take budurwata tana dauke da juna biyu kuma zata haifar mu da yaro"

"Yana dauke da facin rai amma da na mika masa kyuatar sai ya huce" inji John.
Wata yar uwan matar da aka yi ciki ta nuna facin ran ta ga mijin wanda ya amshi kyuatar motar kerar Marcedez benz G-wagon.

"Yan Nijeriya baza su taba daukan mazan mu da daraja. Ta yaya mutum zai amshi kyuata daga wanda yayi ma matar sa ciki? hakika zai kara aikata hakan kuma ya kara siya ma dakikin miji sabon mota. Gaskiya ya bata mun ra i" tace.
Shidai mijin wanda ke tsakiyar kwamacalar yayi tsokaci game da lamarin inda yace sun daidaita ne cikin aminci.

"Kira na da sakarai bai dace ba, hakikani gaskiya baza mu iya sauya abun da ya faru, mun tattauna ne a matsayin mu na maza domin samun matsaya.
"na yafe mai, tun ba yau ba nake mafarkin samun irin wannan motar kuma gashi ya zo mun a sauwake.

"Za'a haifi yaron kuma zan kula da shi tamkar nawa amma idan uban yana son daukan shi zuwa kasar sa Nijeriya ba zan hana shi ba. Zan cigaba da kula da matata domin ina mai matukar son ta. Ni dai ba zan rabu da ita ba domin ta samu juna biyu, ba haka aure yake ba" yace.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: