Wednesday, 22 November 2017
WATA SABUWA A GARIN GUSAU: Wata Ta Dabawa Mijinta Kwalba

Home WATA SABUWA A GARIN GUSAU: Wata Ta Dabawa Mijinta Kwalba
Ku Tura A Social Media

Daga Sani Twoeffect Yawuri Da Jabir Aree Jega

Wata matar aure a garin Gusau na jihar Zamfara ta buga wa mijinta kwalba a kansa daga bisani ta yi amfani da tsinin kwalbar ta caka masa shi a kirji.

Idan ba a manta ba, kwana biyu da ake cigaba da Allah wadai akan matar da ta kashe mijinta a Babban Birnin tarayya Abuja, a yau kuma a babban birnin jihar Zamfara wato Gusau a yankin Tudun Wada, Filin Jirgi Area, wata matar mai suna Murjanatu, ta mamayi mijinta mai suna Bilyaminu Yusuf  ta hanyar buga masa kwalba akansa sannan tayi amfani da tsinin kwalbar ta daka masa a kirji. Inda a yanzu haka Jami'an lafiya na ci gaba da kokarin ceto ransa.

Masu karatu me za ku ce kan wannan?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: