Sunday, 26 November 2017
Wata Mata Ta Kashe Danta A Jihar Katsina

Home Wata Mata Ta Kashe Danta A Jihar Katsina
Ku Tura A Social Media

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Wata matar aure ta hallaka danta ta hanyar shar da shi guba a lokacin da take ba shi ruwan sha, yaron dan wata daya da kwana goma ya gamu da ajalinsa ne ta hanyar shan guba da ya yi daga wajen mahaifiyarsa.

Matar mai suna Rabi’atu Nura mai shekaru 28 mazauniyar kauyen Mazoji daga karamar hukumar Mai’addua da ke jihar Katsina ta hallaka danta Kamaludden Nura mai kwanaki 40 kacal a duniya ta hanyar shayar da shi guba.

Matar ta bayyana cewar ta shayar da dan nata ne ta hanyar ba shi ruwan sha, daga bisani an harzatar da yaron zuwa asibitin Mai Addua domin ceto rayuwarsa kana aka sauya masa asibiti zuwa babban asibitin Daura bayan da jikin ya yi tsanani, dawo da yaron gida ne kuma yaron ya rasu da misalin karfe daya 1:00 na wannan ranar.

Rabi’atu ta ce a lokacin da take baiwa jaririn nata ruwan sha ashe hanunta akwai guba a jiki ba tare da ta sani ba. ta bayyana cewar kisan na jaririn nata bisa tsautsayi ne ba wai da gangan ta aikata ba. ta shaida cewar kuskure ne ya santa hakan ba wait a yi da gangan ba, a cewarta bata da wani matsala ko damuwa da jaririn.

Rundunar ‘yan sandan jihar dai ta sanar da kame matar aure, inda ta bayyana cewar tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda kuma za su ruhumeta da laifin kisan rai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: